Tuesday, January 22, 2019

WASIYYAR WANI UBA ZUWA GA DANSA! KO MEYE HADIN MUTUN DA DABBA!!!

*BABANA YA CE NA JE WAJAN DABBOBI GUDA HUDU BAYAN YA MUTU!!!.*
"Data Alhasan Halliru Kaura"

Wani Bawan Allah yayi wa Dansa nasiha da
Da yaje wajen wasu Dabbobi guda (4) Amma kar yaje sai bayan ya mutu!!!.

Dabbobin da ya umarce shi yaje wajen su- sune:-

1- Doki.
2- kiyashi.
3-Maciji.
4-Kare.

Bayan mahaifinsa ya
Rasu sai ya fara zuwa Wajen Doki yace, Baba yace in ya mutu in zo
Wajen ka, Doki yace Baban ka yana da hikima, kasan abinda
Yasa yace kazo
Waje na?

Yace a'a Sai Doki yace kalli inda nake zaune ya
Duba yaga wajen duk ya baci da kashinsa, Ga jikin sa duk datti, Sai yace kalli wancan
Matashin dokin👉🐴
Sai yaga wajensa a share anyi masa Wanka ga ciyawa mai
Kyau  da ruwa- a gaban sa, sai Doki yace  kaga yanzu ni Na tsufa bani da wani
Amfani shiyasa-aka Kyale ni a wulakance, Shi kuma Matashin
Doki yana da karfin jiki, Ana da bukatarsa shiyasa ake kula dashi dan haka BabanKa  yana yi maka Nasiha da ka mori Kuruciyar ka wajen Abinda zai amfane ka,
Domin lafiyar ka da Kuruciyar ka mutane Suke bukata inka Tsufa ba ruwan kowa da kai.

Daga nan sai yaje wajen kiyashi 🐜yai
Masa bayani kamar Yanda yaiwa Doki- kiyashi yace, zo muje sukaje wajen mushan
Kyankyaso, yayi kokarin ya jawo shi shi kadai ya kasa, sai yaje ya kirawo yan'uwan sa, suna zuwa suka janye Shi.
yace Baban ka
Yana nufin komai
Zaka yi ka hada kai Da yan'uwan ka karkayi kai kadai.

Daga nan sai yaje wajen Maciji 🐍 ya Tarad dashi a cikin
Kogo a la6e yace, yanzu ma, yunwa nakeji, da zan futa a ganni
Kashe ni za'a yi, sai Dare yayi sahu ya dauke, nake futa, ba Wani abu, da ya jawo min wannan bakin Jini sai Bakina da
Harshena😛

Babanka yana nufin ka iya
Harshan ka, ka kiyayi barin zance.

Daga nan sai yaje wajen kare🐺 shima
Yai masa bayani, sai yace, zo muje cikin Gari, suna zuwa sai Yara suka fara jifan
Kare, da kyar suka sha, sai kare yaja shi
Wajen mafarauta suna Zuwa sai Suka fara Murna suna kiran sa
Da sunaye kala-kala Wannan ya jefa masa Nama wannan yana Shafa Shi yana Dariya😀😀.
sai kare Yace Baban ka yana
Nufin ka-kasance cikin Wadanda suke sonka Kuma, ake ganin
Mutuncinka, kuma Aka san  Darajar ka, Kaga misali a kai na.

Allah yasa mu Amfana.

Ameen ya Allah

Abu Woman Danja
Social Media Strategists

Monday, January 21, 2019

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!! KULLU NAFSIN ZA-IQATUL MAUT!!!


Aranar Asabar dindan ta gabata An yi wa ni babban rashi a garin Sheme, inda angon da aka daurawa aure tare da wasu daga cikin danginsa suka gamu da ajalinsu duka bayan kammala daurin aure.

An yi wani mummunan hadarin mota a ranar Asabar da tagabata a kan hanyar Sheme zuwa Funtua cikin karamar hukumar Faskari jihar Katsina, inda hadarin ya rutsa da angon da aka daurawa aure, da yayarsa mace da wansa da kuma wasu duk a kan hanyarsu ta zuwa Funtua bayan kammala daurin aurensa tare da na kanwarsa. Allah ya gafarta masu Ameen.

Mutane da dama a kafar sadarwar ta zamani musamman Facebook da WhatsApp na ta ci gaba da nuna alhininsu game da wannnan irin mutuwar fuju'a da ta afku ga wannnan amgon da a randa ake murnar saka shi dakin angunci, sai gashi zai tsinci kansa cikin dakin kewa na har abada.

Kwamrad Babangida Aliyu Sheme (Zamani) wanda shima dan uwa ne ga marigayen ya rubata cewa:

" Yan'uwan mu da Allah ya yi ma rasuwa jiya sanadiyar hadarin mota jiya Asabar akan hanyar su ta zuwa Funtua daga Sheme.

Wadanda suka rasu sun hada :

😭Hajiya Rakiya kanwar baban mamatan

😭Sadi Muhammad Angon da aka daurama auren jiya

😭Abubakar Muhammad kanin Angon

😭Wani danuwansu daga Funtua .

 Za a  yi jana'idarsu yanzu a garin Sheme .

Allah ya jikansu yasa Aljanna ce makoma a garesu, su kuma yan'uwa da abokanin arzuki Allah Ya bada hakurin jure Wannan Babban rashi. Ameen .

Abu Aiman Danja
Social Media Ta'aziyya.

Saturday, January 19, 2019

NIDA DALIBA

NIDA D'ALIBATA
"" da sauri mommy ta yi gunsa tana salati,sa'ada kuwa kuka ta saka."
Kabeer ne yyi hanxarin dakko swan mai sanyi yadunga kwaraya masa ,cikin ikon Allah yasa ki ajiyar zuciya hade da bude idonsa.
"Sannu kawai su mommy ke masa da su sa'ada ."
Ahankali yatashi zaune ya karbi sauran swan din yashanye sannan yatashi batare da yayi magana ba yyi part dinsa.
      Kabeer ne yyi saurin cewa momm yko maje hospital adubasa dan Allah. Wani mugun kallo sir Aliyu yajuyo ya aikowa kabeer hade da cewa kai yaushe nafara wasa dakai?
Sunkuyadda kai kabeer yyi yace yi hakuri yaya.
"Tsaki sir Aliyu yyi yabar gun", mommy kuwa hararan kabeer tayi hade da nufa part dinta"".
Tana zuwa ta bincikowa sir Aliyu magunguna harda na bacci  sannan ta wuce kitchen ya had'a masa tea mai kauri ta nufi part dinsa.
" shikuwa sir Aliyu kwance yake kan bed yyi rigingine idanunsa alumshe yana tunanin Hafsat dinsa mommy ta sh igo d'akin."
    Saida tayi sallama sau3 tukum ya amsa yana dan Sosa kansa."ahankali mommy ta ce tashi zaune babana! Bbu musu yatashi ta bashi tea din ,bayan yasha tabasa magani ,hade' da yimai nasiha yyi biyayya ga daddynsa kuma yyita addua."
Bajimaba da shan tea din bacci mai nauyi yyi gaba dashi.mommy ta kallesa cike da tasayi tabar dakin.
******************
Hafsat kuwa tun bayan Sir Aliyu yatafi takoma dakinta ta cigaba da aikinta wato kuka.
   Domin itadai kowama zata aura wlh tana tsoron sex dan tanaji in mate dinsu na bada labari in sun karanta a littafi ,cewa da wahala sosai,saitaji duk ta tsorata da aure to Balle batasan wanne marar imanin zaa aura mata ba.tana kukan da tunane tunane had'e da fushi da sir Aliyu bacci yyi gaba da ita, bata farkaba sai gab da sallar la'asar bayan tayi sallah ,tajima tana adduar allah yazaba mata abinda yafi alkhairi yakuma baiyana mata mahaifiyarta.
Cikin ikon Allah saitaji damuwarta ta rage ,nan taje tayi wankanta ta wuce islamiya kasa.cewar yanzun hadda take,amma fa tayi fushi da sir Aliyu sosai.
Bangaren sir Aliyu kuwa shima sai bayan laa'asar yatashi ,yyi wanka hade da sallah.
Cikin ikon Allah yaji duk wani k'unci da damuwarsa sun rage .
   "Neman guri yyi ya zauna yafara tunani n Hafsat dinsa." mur mushi yyi daya tuna duk abinda yakeso matar dazai aura takasance dasu Hafsat tanadasu du ka.nafarko ya. Yana son wacce zai aura takasance yarinya danya sharaf,yadda zai raineta da kansa zai koya mata sonsa da kula da yaransu su zauna lfy.sannan kuma mai kunya ilimin addini da tarbiyyamai son danginsa,sai yaduba yaga Hafsat duk ta had'a wa inna abubuwan. Wata zuciyar ta ce kanada tabbas din zaka mallaketa?
Tunawa yyi kilama har yanzun batadena kukaba da sauri yazaro wayarsa yakira baba.
bbu bata lokaci baba yadaga had'e da sallama,Hafsat dke gefensa  cikin sanyin muryarta tace baba waye yakiraka?
Baba dke cewa lfy lau aliyu ya gida?
Atake Hafsat ta gane cewa da sir Aliyu baba keyin waya,aisaita kwanta ta rufe ido kamar me bacci.
Shikuwa sir Aliyu tun sadda Hafsat ke tambayar baba yaji muryarta,dama dan ita yakira yanaso suyi magana.
"can yace baba ko Hafsat na kusa mu gaisa?"
Kallonta baba yyi ,yace aiko kamar tayi bacci Bari natasheta.
Da sauri sir Aliyu yace ah ah baba rabu da ita tayi baccinta.nandai sukayi sallamada baba,sir Aliyu kuwa yasan sarai  Hafsat ba bacci takeba kwaidai fushi take dashi.
      Murmushi yyi yace oh Hafsat akwai rigima da shagwaba ,nasan haka zanta fama da rigimarta inmukayi aur......da sauri yyi shiru sakamakon tunawa da yyi Hafsat wani za'a aurama ita.
" cikin jin haushi hade da wani kishi da yataso masa yatashi yafita dan xuwa masjid.
Koda dare Hafsat da sir Aliyu bbu Wanda yyi baccin kirki duk da damuwa suka kwana ,kowa na tunanin dan uwansa.
Washe gari haka sir Aliyu yatashi duk yad'an fad'a saidai fuskarsa tayi fiyau da shi,ko break beyiba yanufi gidansu hafsat ,dan hankalinsa yak'i kwanciya Hafsat tana fushi dashi.
Yana isa yyi parking yafito kaitsaye yakutsa kai cikin gidan ,asoro yasami Hafsat tana sharewa kallo daya zaka mata kasan tana cikin damuwa.
Ai tana ganinsa tasaki tsuntsiyar tayi cikin gidan aguje.
Murmushi sir Aliyu yyi dan yalura har yanzun fushi take dashi,dan haka shima yasaka kai cikin gidan...

MATA SUN TAKA RAWAR GANI!!!

a

GUDUN MAWAR MATA A ADDININ MUSLINCI.
A TAHIRIN MUSULUNCI*🧕 MACE CE* TA FARA MUSULUNTA* a duk duniya kuma ta yiwa musulunci hidima da dukiyar ta da duk abinda ta mallaka harda GwalaGwalanta *(NANA KHADIJA) (R.A)*

*🧕MACE CE*
   Sanadiyyar samun Taimama a shari'a *(UMMUNA A'ISHA) R.A*

*🧕MACE CE*
    Ta ilmantar da Sahabbai bayan wafatin Annabi{s.a.w}
 *NANA A'ISHA (R.a)*

*🧕MACE CE*
   Sanadiyar tsiran sahabbai daga fushin Allah sanda akai sulhun
*HUDAIBIYYA* Kuma *MACE* ce ta shawo kan *SAHABBAI* har suka tsira daga  fushin Allah.*(UMMU SALAMA) R.A*

*🧕MACE CE*
   Ta Kwantarwa Manzon Allah *HANKALI* Lokacin da aka kikiran karya da aka yiwa A'ISHAT, kafin saukar wahayi *(BARIRA) (R.A)*

*🧕MACE CE*
  Sanadiyyar shigar mutum Aljannah  Wanda Manzon Allah *{S.A.W}* yace idan mutum ya tarbiyyantar da
ita koda bashi ya haife ta ba, zai shiga *ALJANNA* shi da Manzon Allah *{S.A.W}*

*🧕MACE CE*
   Ta zamo Ma'aunin da mai Aure zai gwada kimarsa agun Mahaliccinsa, idan ya kyautata mata yana da sakamako mai kyau, idan kuma ya cuceta akwai uquba daga Allah.

*🧕MACE CE*
   Shari'a ta tanadar *MATA* Ladan Jam'in Salloli guda biyar (5) Da Juma'a da Jana'iza da Jihadi duk ba sai taje ba amma sanadiyyar ta Kyautatawa *MIJINTA* Allah Zai bata duk *LADAN* wadannan Ibadun.

*🧕MACE CE*
    Sanadiyyar warware matsalar Zihari, suratul *(MUJADALA)*

*🧕MACE CE*
      Ta fara yin Sa'ayi tsakanin *SAFA da MARWA (HAJARA)*

*🧕MACE CE*
     Sanadiyyar tsiran mutanen sarauniyar Saba, suratul *(NAML)*
*BILKISU MAI GADON ZINARI*

*🧕MACE CE*
    Sanadiyar musuluntar Sayyiduna Umar *(R.A) (FATIMA)*

*🧕MACE CE*
     Ake samun nutsuwa da ita! *LITASKUNU ILAIHA* Namiji ba zai taba samun sukuni ba sai yana da mace!

*🧕MACE CE*
      Duk mulkin mutum da dukiyar shi sai da ita yake kara kima a idon mutane!

*Mata iyayenmu ne Mu girmamasu!*

Abu Aiman Danja
Ocial Media Fadakarwa

Thursday, January 17, 2019

MATSALOLIN MASU GOGORIYON YIMA YARAN ISLAMIYYA WALIMA

Matsalolin Masu gogoriyon yima Yaran Islamiya walima

Daga Abu Sadiq Muhammad Bello

A gaskiya karatu yanzu ya zama abinda ya zama musamman a kasashen Hausa
Saboda son zuciya dake tattare da wasun mu dalibai da wasu daga cikin iyayen mu
Gaskiya na zabi wannan maudu'i ne saboda illa da hakan ke haifarwa yayi yawa

★Bari mu ga wasu daga cikin dalilan da yake sa wasu Malaman islamiyoyi ke RUSHING din Yara don ganin sunyi Masu walima

1-Azazzalawan iyaye da gaggawa wajen ganin yaransu sun sauke al-Qur'ani
2-Cire Yara daga duk islamiyar da ba a yima Yara walima duk shekara
3-San abin duniya daga wasu daga cikin Malaman
4-Rashin me da hankali a kan karatu

Wadannan wasu ne daga cikin dalilan da suka sa wasu islamiyoyin mu suke tunkuda Yara a karatu don ganin anyi sauka da wuri

★Yanzu za mu duba muga wasu daga cikin illolin da hakan ke haifar mana
1- a al'adar kasan Hausa kashi saba'in (70%) na Yaran da ake yima walima basu ci gaba da karatu musamman MAZA
To zaka ga yaro ya bar islamiya bayan sauka amma baze iya karntar da wani al-qur'ani ba
2-Zaka ga tun ana sauran wata daya ko biyu za a yankan ma yaro ayoyin da ze karanta ranar walima amma in ranar tazo ya hau mimbari se ka ga yana Jan ayar itama tana Jan shi
3-Hakan ya janyo mutane da dama basu San darajar karatu ba sun dauka makarantun da ake walima akai akai sunfi karatu
4-Kuma hakan ze janyo karancin kwararrun malaman da zasu karantar kuma su rike islamiyoyinmu a nan da wasu shekaru Masu zuwa

★Shawarwari ga iyaye, malamai da kuma mu dalibai akan wannan mas'alar

*IYAYE
1. Ya kamata ku Zama Masu taimakama malamai wajen kula da karatun Yara ta hanyar hada Masu extral timetable da zaku dinga duba Masu darrusan da ake Masu a Makaranta da kara Masu haske akan ababen d basu fahimta ba a Aji
2-Yakamata iyaye su tabbatar suna tura yaransu Makaranta a kan lokacin da hukumar Makaranta ta ajiye na zuwa Makaranta
3-Yakamata iyaye Sufi bada muhimmanci wajen lalubar wace Makaranta aka fi karantarwa ba Wai makarantar da akafi yima Yara walima ba
4-Siya ma Yara duk abinda suke bukata na karatun
5-Nuna ma Yara a shirye kuke Ku kashe Masu ko nawa ne matukar kuna da hali don ganin sunyi karatu
6-Bama malamai cikakken goyon baya don su karantar da Yara

*YARA
1-Muji tsoron Allah mu mai da hankali akan karatunmu
2-Mu dage da rokon Allah ya fahimtar damu ababen da ake koya mana
3-Mu girmama malamanmu

*MALAMAI
1-Kuji tsoron Allah Ku kawar da kai daga ababen da ake samu lokacin walima
2-Duk Wanda ya bude islamiya ya kamata ya zama yana da tsarin da yake tafiyar da karatunsa akai kuma karya bari wani yana juya akalar karantarwarsa
3-Ya dinga samun lokaci Koda sau daya ne a duk bayan wata uku yana gayyatar taro yana tattaunawa da iyayen yara don in akwai wata matsala anan yakamata atattaunata a samu mafita
4-Kada ayi ma yaro sauka har se ya sauke alqur'ani sauka na haqiqa ta yanda duk Inda aka bude masa ze karanta babu fargaba kuma babu gargada
Sannan ya taka matakai kamar haka
1. A kalla ya haddace arba'una Nawawi a bangaren hadisi
2. A bangaren tauhidi ha sauke usulussalaasa
3. A bangaren Tajwidi ya sauke kuma ya haddace tuhfatul atfaal
4. A bangaren fiqhu ace ya sauke kuma ya San akhdariy yadda ya kamata
5. A bangaren lugah ace ze iya rubuta wasika da larabcin
6. A bangaren sirah ace ya kammala Khulasatun nuurul yaqiin na farko
7. Sannan dole ya kasan ce yana da hadda karancin izu biyu

Wallahi duk makarantar da ta dauki wannan tsari kuma tasa shi a cikin tsarin makarantar kuma duka iyaye su rattaba hannu a wannan to a walimar su na farko za ayi mamakin irin hazikan Taliban da zasu have duk da dai nasan baza suyi yawa ba amma ai da haihuwar yuyuyu gwara daya kwakkwara
Kuma da ace irin wannan tsarin malamanmu suka yi amfani dashi tun muna islamiyah wallahi da yanzu mun wuce haka nesa ba kusa ba

Ina rokon Allah ya bama malamanmu ikon amfani da wannan shawarwari domin kannanmu Masu tasowa su wuce wannan mataki da muke kai amin.

Abu Aiman Danja
Social Media Strategists

📝Bincike/nazari da rubutawa📝
Abu-Sadiq Muhammad Bello #Al_Baiquniy

Tuesday, January 15, 2019

GYARA KAYAKA BAYA ZAMA SAUKE MU RABA BA!



TSOKACI, GYARA KAYANKA....

👰Idan Mace na wahalar da Namiji sai ace kawai sake ta auro wata. Amma idan Namiji na wahalar da Mace sai ace ta yi hakuri Aljannar ta na Karkashin kafar mijinta.

👰Mace ta yaye tsiraicinta saboda rashin tsoron tsinuwar Allah amma ta rufe tsiraicinta saboda tsoron sanyi.

👤Namiji ya gama yawon neman matan banza a waje, amma idan ya zo aure ya ce Ustaziya ya ke son aura.

👰Mace ta fifita biki akan ba wa mijinta cikakkiyar kulawa idan ya so kara aure ya zama Namiji Dan kunama.

👥Maza su zauna a majalisa suna fadin 'ya'yan unguwa wance da wance sun lalace amma idan dare ya yi sune abokan shakatawarsu.

👰Mace ta gama yabon 'yar makota 'ga hankali ga tarbiyya amma ba mijin aure abin tausayi ga ta marainiya'. Da mijinta ya so aurenta ya zama mara amana.

👤Namiji ya kashe kudade a wajen cin abinci yana fadin 'Da yadda mata suka iya makeup haka suka iya girki da mun ji dadi' amma ya bar gida da miyar kuka.

👰Mace ta gama zagin Uwar Miji, amma idan ta haifi da matarsa ta mallake shi tace bata yarda ba asiri ta yi masa.

👤Namiji ya auri Mace tagari ka gan shi ya tare a otal da 'yar bariki, idan ka tambaye shi ya ce ba ta iya soyayya ba. Idan ance ya auri wannan ya ce 'yar iska ce.

👰Mace ta rika kwana da mazan wasu a otal amma tana fadin idan ta yi aure ta kama mijinta da wata kashe ta zata yi.

👤Namiji ya yi shekara da shekaru yana bin gidan Budurwa ayi da shi ya fito yace bai shirya ba, amma idan ya gan ka wajen kanwar sa yana cewa ka fito ka ce ba ka shirya ba, zai yi maganin ka.

👰Mace ta ce da kishiyar gida gara ta waje amma idan ta haifi mace so ta ke yi a aure ta.

👤Namiji ya rika ihun Soyayya sai su Kareena amma a Gida ya kasa zama Sharukhan.

👰Mace ta tsangwami Mijinta da zagi da gori ya kasa tsinana mata komai a rayuwa, 'in banda kaddara me zai sa na aure ka? Amma da ya fadi ya rasu sai ihun yanzu yaya zan yi ya mutu ya bar ni da ya'ya?

👤Namiji ya dage Mace fara ko mayya ce, amma ya cika sohiyal midiya da ihun Mata sun lalace da bilicin.

👤Namiji na cikin bakin talauci ci da kyar sha da kyar ba kudin kai yara makaranta, amma Mace na addu'ar gara su zauna a talauci da ya samu arzikin kara aure. Allah ya bada ikon Gyarawa Amin.

Abu Aiman Danja
Social Media Fadakarwa
15/01/2019.

Monday, January 14, 2019

KUTASHI TSAYE! KUYI HATTARA DUNIYA MAKARANTA (IYAYE)

KU TASHI TSAYE! KUYI HATTARA DUNIYA MAKARANTA (IYAYE)!!

A shekarun da suka gabata, talakawa masu karancin ilimin Addini da na Boko, masu tsananin Talauci sun rayu da iyalansu cikin hali na babu da tsabar wahala a rayuwa. Amma ya'ya'nsu sun sami damar yin karatut-tukan Boko da Addini, akasamu da yawa daga cikinsu sun zamo:

a. Likitoci (Doctors)
b. Injiniyoyi (Engineers)
c. Ya'n kimiyya da fasaha (Scientists)
d. Akowuntoci (Accountants)
e. Lawyoyi (Lawyers)
f. Masu Zane-zane (Architects)
g. Farfeso-shin ilimi (Professors). Wadan nan nakira su da group 'A'.

Ya'n group 'A' yaran da sukayi Gwagwar-mayar a karan Kansu bayan kammala Primary aji shida ko grade 12, suka zamo mahimman mutane a yanzu. Mafiyawan su sun:
👉 Je makaranta makaranta a kasa da kafafun su
👉 Je gona aikin kodago Dan abincin da zasu ci ko iyayen su.
👉 Debo Ruwa da Iccen konawa a kawunan su.
👉 Farawtar Namun daji.
👉 Wasu ayyukan kamar kasuwanci da kira da dai sauran su.

Ayanzu group 'A', wadan da suka zama IYAYE a yanzu, suka Samar da ya'n group 'B' ya'ya'nsu.
Wadan nan ya'n group 'B' yara ne masu;

✅ Gata gaba da baya
✅ Ana yimasu duk ayyukan dake cikin gida tin suna  yan Nursery Har zuwa karatun gaba da sakandary
✅ An Sanya su a makarantun kudi mai tsada ko kuma an tura su kasashen waje domin suyi karatu
✅ Suna iya kallon movies tin daga safe Har Dare a Ranakun hutun mako
✅ Ana basu kulawa kamar yara jarirai ko Sarakuna ko ya'ya'n Sarakuna
✅ Basayin wani aikin gida komin kan-kantarsa
✅ Abinci da zasu ci sai an ajemasu shi a tebirin cin abinci
✅ Kwanon abincin ma sai andauke kuma an wanke a gidan
✅ Ana basu Manyan motoci da kaya masu tsada
✅ Ana basu kudin Sawa aljihunci ba tare da sun bukata ba
✅ Iyayen su ke taimakon su wajen yin Assignments
✅ Duk da haka ya'n kadan ne a cikinsu ke iya karatu da rubutu.

Ya'n group 'A' sun kula da iyayen su, da ya'ya'n su , Group 'B', ya'yan su suna nan suna gwagwarmaya su gaje su suna ya'n shekara 30!!

Amma kuma Abinda yazamo masu abu mai wahalar gaske sabo da  sukayi a rayuwrsu komai sai antaimakesu kuma taimakon daga ya'n group 'A'. Don haka yakasance basa iya taimakon kansu da kansu, iyayensu ko kuma al'umarsu. Sun kyale iyayen suna horar da wasu yadda za'a sami duniya.

Me karatu a wane group kake?
❎ A rage ji-ji da kai da taimakon da baizama dole ba ga yara!
❎ Ka taimaki ya'yanka su tashi da wayansu da hikimarsu da kaifin kwakwalwarsu domin tunkarar kowane kalu-bale na rayuwar su lokacin da baka/ki
❎ Barsu su tinkari gaskiyar al'amari na rayuwa. Koya masu yadda zasu girma suna dogaro da Kansu!!

Koyar da ya'yan ka/ki ;
✅ Jin tsoron Allah
✅ Su girmama na gaba kada su raina kowa
✅ Koya masu jajircewa da dogaro da Kansu a rayuwa

Iyaye Ku hukunta ya'yanku in sunyi ba dai-dai ba domin su girma suna masu kare mutuncin kawunan su daku baki daya kuma su zamo masu anfani ga al'umarsu ba mararsa amfani ba ga kawunansu da Al'umarsu.
Allah ka shirya mana zuri'ah Amin..


Abu Aiman Danja
Duniya makaranta
15/01/2019.

Thursday, January 10, 2019

"AURE KO MAKARANTA" SAKIN NA HANNU KAMUN NA GUJE!!


 Mafiyawa YAN'MATA da samari a KASAR Hausa a wan nan Zamani Suna tsintar kawunansu cikin wani yanayi mai Hadarin gaske Wanda kai mafi yawa-yawan yan'mata ga yin da nasani!!

Yayin da Saurayi yaje neman auren mace 'yar shekara 18+ mafi yawa daga cikin su haka za su fada maka.

Idan kuma macen ta nuna tana da ra'ayin auren, sai a bata shawara, da cewa: "karatun nan shi ne gatanki, idan ba kiyi ba za ki zama 'ci ma zaune' don haka kada ki yarda, zaki zauna komai sai kin jira mijinki ya miki". Ko ace mata " idan mijinki ya sake ki ko kuma mijinki ya mutu, za ki sami aikin gwamnati, ki dogara da kanki, amma idan ba ki yi karatu ba za ki zama mai bara da maula akan titi"! Data nan sai ta kafe lallai karatu zatayi shi kuma saurayi ya tafi.

Yayin da ta gama karatun, lokacin ta kai shekara 23 ko 24. Lokacin sai burinta ya karu, saboda tana jin cewa, ta kai wani babban matsayi, ta sami shedar DIPLOMA, N. C. E., ko DEGREE. Sai irin mijin da ta tsarawa kanta za ta aure. Samarin da a baya take kulawa, yanzu likafa ta ci gaba,tana ganin tafi Martin su ko kuma ta raina su. Samari suyi ta zuwa, amma ta tsaya ruwan ido, sai mai kaza da kaza (abin duniya) saboda sai ta zaba. Haka za tai tayi har takai shekara 28 zuwa 30 ko 33. Lokacin samarin sun fara tafiya suna barinta, saboda shekarunta sunyi yawa.

Ana cikin haka, sai kuma bukatar auren ta kama ta sosai, ba zato ba tsammani. Saboda lokacin sa'aninta sun hayayyafa, sunyi zuriyya. Ita ce shiga malamai dan neman addu'ar samun miji. Da zuwa makarantun Islamiyyu dan sa yara dalibai su taya ta da addu'a Allah ya kawo mata miji, ta hanyar raba musu biskit da alewa.

Haka abubuwa za suyi ta kasancewa, idan Allah ya taimake ta sai kaga ta auri Tsoho sa'an mahaifinta, ba dan shi take so ba, a'a, sai dan ta rasa wanda take so. Wata kan haka za tai ta zama, har shekara 40 ko 45- Lokacin ta zama ta al'umma, sai dai aikin office (idan ta sami aikin kenan). Za tayi ta samun promotion a wajen aiki, ga kudin ta samu amma ba kwanciyar hankali!!!

Allah ya kiyaye (ba fata ake ba), idan ba ta sami aikin ba, ko kuma ta samu, amma babu miji, ga shi kulkun sha'awar d'a namiji tana damun ta. Wata a nan sai ta kauce hanya, ta fara bin 'yan samari tana basu kudi suna amfani da ita, dan ta sami gamsuwar sh'awarta, wato ta zama (sugar mummy).  Wata kuma ta koma harkar neman mata 'yan uwanta (lesbianism), wata kuma ta zama karuwa mai lasisi, ta hanyar bin ma'aikata, abokan aikinta.  Idan kuma Allah ya so, sai ta zamo me yawan ibada, azumi da sallah. Wan nan shine sakin Na hannu kamun Na guje.

 Hattara mata a yi tunani sosai, aure baya hana karatu, haka zalika, karatu ma baya hana aure. Abi Allah a zauna lafiya.

Abu Airman Danja
Social Media Fadakarwa.

Saturday, January 5, 2019

MAHAKURCI MAWADACI

           MAHAKURCI MAWADACI WATA RANA

1. An haifeka a mafi daukakar asibiti amma ni a gida aka haife ni amma gaba daya mun rayu.
2. kayi makarantar kudi ni ta gwamnati nayi amma mun hadu a jami'a / kwaleji daya.
3. ka kwanta a kan gado na kwana a tabarma amma gaba daya mun wayi gari, kowa ya nufi harkar sa.
4. ka saka kaya masu tsada ni kuma na saka masu arha amma duk mun rufe tsiraici.
5. ka ci jolof rice da farfesun kaji amma ni na sha koko da kosai amma dukanmu mun koshi, Alhamdulillah.
6. ka hau motarka mai tsada ni kuma na hau ta haya amma duk mun isa gurin da muka nufa.
7. wataqila kana karanta wannan rubutun daga wayar Sony xperia, q10, iphone6+ ni kuma ina wannan rubutun daga tsohuwar Nokia x2-01 amma dai wuri daya muka shiga; WhatsApp ko a Facebook.

Ya Ku masu karatu, rayuwa ba gasa ba ce akwai hanyoyi da yawa ta cimma buri.

1. Hanyoyi mabambanta kan kai mutane ga matsaya daya.
Don ka ga makwafcinka yana samun nasara kai ba yana nufin kai baka da nasara a rayuwa ba.

2. Farin ciki ba shine samun duk abinda rai ke buqata ba, Farin cikin shine samun wadatar zuciya da haquri da abinda Allah ya hore maka.

Manzon Allah (S.A.W) yace "yawan dukiya ba shine arziki ba, wadatar zuciya shine arziki"
Allah Ya kara mana wadatar zuci, Ameen.

 Kada kayi gaba da mai son yin gaba dakai,idan ka ganshi kayi masa sallama. Kada ka damu da hassadan maihassada, barshi¬
muguntansa zata koma kansa. "Duk wanda ya ce duniya ita ce mafi mahimmanci a gare shi, To tabbas bakin cikin sa zai yawaita".

Kayi hakuri wurin barin sabon Allah, domin wani abun kanaso amma babu yadda zakayi,hakanan zaka barshi don jin tsoron azabar Allah. "Ba abin alfahari ba ne don ka yi rinjaye ga mai karfi, Abin alfahari shine ka yi adalci ga mai rauni".

 Wanda ya fada maka magana mai zafi, kalma mai daci da 'kuna, mayar masa da tattausa mai taushi kamar ruwan sanyi. "ALLAHU ya bamu ikon ruko da gaskiya!!
 MAFIFICIYAR ZUCIYA: ita ce zuciya sassauka, wacce batta rabuwa da gaskiya.

MAFIFICIN MUTANE: shine mutumin da bai manta dakai har abada. Saboda kaunar da yake yi maka Domin Allah ne.

MAFIFICIYAR RANA : ita ce ranar da tazo ta wuce baka aikata wani zunubi ba.

MAFIFICIYAR KYAUTA : ita ce addu'ar da wani yayi maka ba tare da saninka ba.

Allah nake roko ya yarda dani daku baki 'daya, ya yardar daku, ya yaye muku dukkan bakin-cikinku, ya saukaka muku dukkan lamarinku, kuma ya sanyaku acikin Ahalin gidajen Musulmi Aljannah Aameen.

Abu Aiman Danja
Social Media Strategists.

ME YASA 'YAN SOCIAL MEDIA BASU DA MUHIMMANCI A AREWA?

Me Yasa 'Yan Social Media Basu Da Muhimmanci A Arewa?

Su Suka Jawowa Kansu!

1. Mecece Social Media?
Itace shafukan sadarwa na zamani wanda zasu baiwa mutum damar saduwa da wani ta hanyar rubutaccen sako, hoto, video, ko kira kai tsaye da akeyi. Social media sun hada da facebook, whatsApp instagram d.s.

2. Su Waye 'Yan Social Media?
Idan muka ka kalli ma'anar social media to masu amfani da wadannan shafukan sune 'yan social media, sai dai abin ba haka yake ba, idan akace 'yan social media sune wadanda suke Rubutu a shafukan internet, wadannan marubuta su ake kira a turance da Bloggers.

Yadda Abin Yake A Arewa:-
Daga sanda ka fara rubuta a social media mutane suna jin dadi to sai suyita zuga ka kai ga dan Social Media kullum kayi tayin abinda yake faranta musu koda kuwa abinda kake zai hanaka yin wajibinka na yin kwadagon kaiwa bakin salati.

Idan ka baiwa Mutane rayuwarka kana wannan aikin su kuma babu ruwansu da kana da bukata su dai kawai ka faranta musu duk randa ka gano kuskurenka ka juya zuwa ga fifita neman na halak dinka akan social media sai su fara aibata ka, wannan shine abinda yake faruwa a yanzu.

Abinda Yakamata Dan Social Media Yayi A Arewa:
Ya zama kana da sana'ar ka wadda itace kan gaba a Social Media ta yadda zaka iya rike kanka da ita.
Idan social media ta zame maka jiki kaje ka kashe kudi ka koyi yadda zaka dinga samun kudi ta harkar tunda halastacciyar sana'a ce.

Yaya Abin Yake A Kudu?
A kudu 'yan social media Mutane ne masu daraja a Idon al'umma amman sunyi daraja ne saboda suma sun daraja kansu a lokacin da dan Arewa ya shagala da shafin facebook kadai ka tara followers to sai aka kwace ko aka rufe maka account din Shikenan ka rasa shi?
Kowa ya san facebook na wani ne kaje kake haya kana biyan kudin Data don haka baka da cikakkiyar dama akai!

To su a kudu kowa yana kokarin samar da shafinsa wanda wannan shine darajar Marubuci a Social Media amman yau kaf marubutan APC na Arewa Bashir El-Bash kawai na san yana da shafi a Internet.
Ta Yaya Za'a Daraja ku?

Bari Kuji Ta Inda Bashir Ahmad Ya Faro:-
A shekarar 2010-2012 ina Junior Secondary ina shiga Google nayi research daga cikin bloggers na Arewa wanda nake gani shine Bashir Ahmad yana da wani blog na Wapka (tun ana yin Wapka), kunga kenan Bashir Ahmad Blogger ne kuma ya san komai na Blogging ya san mutum zai iya rike kansa ta blogging.

To don Allah daga wancan lokacin zuwa yanzu cikin 'yan APC kawai da mutum nawa ya dora a hanyar Blogging?

Yanzu kuna ganin inda ya dora su Biyora a hanyar domin suma su inganta rubutunsa ya zama yau in kana neman rubutun da Biyora yayi shekara kaza ka san inda zaka nemeshi kuma a internet ko ina rubutunsa zaije, yawan Followers da Biyora yake dashi da Bashir ya dorashi akai da yanzu Allah ne kadai ya san abinda zai dinga samu, kuma kuna ganin da zama a samu kofar da za'a nemi janyeshi?

1. Linda Ikeji ta fara blogging a 2006 yanzu a duniya idan akayi maganar Bloggers a Nigeria ita take zuwa ran kowa, yanzu shafinta har kamfanunuwa ke bata talla yau ta tsaya da kafarta kuma 'yar social media ce.

Ga sunayen wasu 'yan kudu duka matasa ne da abinda suka rika kenan yanzu sun wuce raini:-
2. Uche Eze Pedro ita tayi BellaNaija
3. Demola Ogundele shi yayi NotJustok
4. Kemi Filani tayi shafin Kemi Filani
5. Emeh Achenga ita tayi MespetitanNigeria
6. Ladun Liadi ita tayi shafin LadunLiadi
7. Noble Igwe me 360nobs
8. Japheth Omojuwa shi a yanzu yana cikin wadanda naganarsu ta zaga duniya dalilin hakan a ganinsu 'yan siyasa biyansa kudi suke don karma yayi magana akansu.

Wani zaice ni me yasa ban nuna musu ba?
Duk mai bibiyata yaga yanda nayi ta babatu akai kuma har mutane na nema duk mai sha'awar na koya masa kuma wanda suka ce suna bukata sun gani yanzu haka suna nan munayi wajen 100+ sun fara blogging 'yan arewa.

Allah ya kyauta.

Abu Aiman
Social Media Strategist.

Tuesday, January 1, 2019

YAN MAZAN JIYA A KASA NIGERIA (TARIHIN SIR ABUBAKAR TAFAWA BALEWA)




TARIHIN SIR ABUBAKAR TAFAWA BALEWA

SIR. ABUBAKAR TAFAWA BALEWA

  An haifi marigayi firimiyan Nigeria na farko watau Abubakar Tafawa Balewa a garin Tafawa Balewa na Bauchi, a shekarar 1912.
   Mahaifinsa Yakubu ɗan Zala ya fito me daga kabilar Bagire, kuma shine dagacin Lere.
  Tafawa Balewa ya soma karatun alkur'ani dana boko a Bauchi, koda yake ance yaje katsina karatu, daga bisani ya samu gurbin karatu a Barewa Kwalegi dake zaria, yana kammalawa kuwa aka bashi shaidar malinta inda ya dawo Makarantar Midil ta Bauchi ya soma koyarwa.
  Malam Tafawa Balewa ya samu damar gurbin tafiya Ingila karo karatu tare dasu Malam Aminu kano, inda ya samo shaidar Malanta na koyar da Tarihi acan, sannan ya dawo gida Nigeria.
  Da dawowarsa kuwa sai ya zamo wakilin turawan mulki masu kula da makarantu, alokacin kuma an ruwaito yana cewa ya gano yadda rayuwa take tafiya a turai cikin 'yanci da walwala, kuma ya haɗu da mutane masu bin doka ba tare da tsoron komai ba, don haka yana kallon Nigeria da wani yanayi na daban.
  A lokacin ne ya soma kafa kungiyar malamai ta Bauchi, inda suke tattauna hanyoyin samar da cigaba, daga bisani kuma ya tsaya takara kuma yaci zaɓen ɗan majalisar wakilai na Arewa a shekarar 1946.
  A majalisar Arewa suka haɗu da Ahmadu Bello har kuma suka kafa jamiyyar 'Northern People's Congres' watau NPC.
   A shekarar 1952 tafawa Balewa ya zama ministan aiyuka, daga baya kuma ministan sufuri.
 A shekarar 1957 aka naɗa shi babban minista, sannan kuma bisa haɗin guiwar jamiyyarsa ta NPC da jam'iyyar Nnamdi Azikwe, Tafawa Balewa ya zamo Firimiyan Nigeria na farko bayan karɓar 'yancin kai a shekarar 1960. Kuma ya sake tsayawa takara a shekarar 1964 ya lashe zaɓe.
  Ana yiwa Tafawa Balewa lakabi da 'Golden Voice', saboda nasibinsa wurin iya zance da gamsar da mutane. Kuma a wancan lokacin, ya zamo fuskar Afirka, domin yayi aiki tukuru wajen haɗa alaka tsakanin Nigeria da kasashen Afirka, da kuma warware matsaloli tsakanin Kasashen Afirka. Sannan ya cusa 'yan Arewa da dama acikin kunshin mukaman Gwamnatin tarayya.
  Akarshe, lokacin Juyin mulkin 17 ga watan janairu na shekarar 1966, ance wasu sojoji su biyar sun kutsa kai gidan sa inda suka sace shi.. Daga baya kuma aka tsinci gawar sa.
   Da fatan Allah yajiqansa Amin.

Abu Aiman 
Social Media (Tarihin Yan Mazan Jiya)

IN-KAJI WANE BA BAN-ZABA (TARIHIN MAITAMA SULE DAN MASANIN KANO)

IN KAJI WANE BA BANZA (TARIHIN MAITAMA SULE DAN MASANIN KANO)



MAITAMA SULE DAN MASANIN KANO

An haifi marigayi Yusuf Maitama Sule ɗan masanin kano a ranar 1 ga watan Oktoban shekara ta 1929 a birnin kano.
   An sa masa suna Yusuf ne, saboda sunan Mahaifin Madakin Kano Mahmudu, don haka Madaki yana kiran sa da suna Abbana. Sunan Maitama kuwa an sanya masa shine sabili da Galadiman Kano Yusuf, saboda an yi amfani da makamai sosai lokacin yakin basasar Kano, don haka ake kiran duk wani Yusufu da suna Maitama a wancenn lokacin.
  Madakin Kano ya yi wa Mahaifin Maitama, Abba Sule Danmuri, mukamin mai kula da dukkan al'amuransa na gida da kula da Dawakai.
   Maitama Sule na ɗan shekaru 4 mahaifiyarsa Hauwa wacce ake kira 'Yarkayi ta rasu. Ita kuwa Allah yayi tane mace mai ban dariya, mai raha, ba ta fushi, shi ya sa duk bukin da ya tashi ita ake kira ta yi ta magana a gidan buki, halinta da iya maganarta Maitama ya gado.
  Madakin Kano ya saka Maitama Sule a makarantar Elemantare ta Shahuci a cikin watan Janairu, 1937, dama tun kafin akai sa makarantar boko, suna yin karatun alkur'ani a gida.
   A ka'ida shekaru huɗu ya kamata ayi a elemantare, amma saboda hazakar da Maitama Sule ya nuna shekaru biyu kacal yayi aka bashi damar ɗaukar jarabawar zuwa midil wato mataki na tsakiya.
  A wancan lokacin ne kuma Maitama Sule ya fuskanci kalubalen da bai taba fuskanta ba a rayuwarsa kasancewar a lokacin ne mai ɗaukar ɗawainiyarsa a rayuwa ya rasu cikin shekarar 1939. Aka bar kujerar Madaki, tsawon shekaru biyu, ba'a naɗa kowa ba, har sai a shekarar 1941.
  Bayan haka ta faru, sai Gaba ɗaya ɗawainiyyar Maitama Sule ta koma kan Mahaifinsa Abba Sule, wanda a wancan lokacin kuma ba shi da karfin da zai iya ɗaukarta. Sai da ta-kai Abba Sule, ya saida duk wani abunda ya mallaka har da suturunsa na sawa dan ya ɗauki ɗawainiyar 'ya'yansa, a lokuta da yawa haka suke kwana da yunwa.
  Ranar da suka samu ɗan abin taɓawa, a daren gasasshehen rogo ne za su ci su kwanta. A karshe Maitama Sule ya shiga makarantar Middle, a wannan datsen an kai matsayin da Maitama ko suturar da zai sa ba shi da ita, kayan makaranta kawai sune kayan sanyawarsa.
  A shekarar 1943 Maitama ya shiga kwalejin Kaduna, yana ɗan shekaru 13. Maitama, ya kammala karatunsa na kwaleji cikin shekarar 1948, ya kuma kama aikin Malanta, a makarantar Middle ta Kano.
  Maitama Sule ya tsaya zaɓen majalisar wakilai, yana takara da  tsohon Malaminsa a makaranta, watau Malam Aminu Kano, wannan zaɓe ya gudane a Central Office, wannan abu ya faru ne a 1954.
  Lokacin da aka faɗi sakamakon zaben Malamin, zaɓen ya bada sanarwar cewa Maitama Sule ne ya lashe wannan zaɓen.
 Ana fadar haka kuwa sai Mallam Aminu Kano, ya juyo ya cewa Maitama Sule: ina tayaka murna, saura idan kaje kuma ka ba mu kunya.
   Maitama Sule ya cewa Aminu Kano, "Yallaɓai wallahi, ba zan ba ka kunya ba". Suka riko hannun juna suka fito tare, wanda suka fara gamuwa da shi shi ne Ado Bayero, inda ya rike hannun Maitama Sule, ya nufi inda magoya bayansa suke, ya ce sun ci zaɓe.
   Maeigayi Maitama Sule Ya zama ministan tama da karafa a janhuriya ta farko. Sannan Bayan faɗuwar jamhuriya ta farko, ya dawo gida Kano, inda ya rike mukamin kwamishinamai kula da kananan hukumomi a gwamnatin Audu Bako. Ya rike mukamin shugaban hukumar sauraren koke-koken, jama'a ta kasa a gwamnatin Msrigayi Janar Murtala.
Yayin da a shekarar 1979 ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar NPN, sai dai Shehu Shagari ne ya lashe zaben.Har ila yau, gwamnatin Shagari ta naɗa shi jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya watanni bayan kammala zaben.
A can ne kuma ya jagoranci Kwamitin Musamman kan Yaki da Wariyar Launin Fata na majalisar, wanda masu sharhi ke ganin ba karamin matsayi ba ne.
  Hakazalika, bayan da Shugaba Shagari ya lashe zaɓe a shekarar 1983 ya sake nada Maitama Sule Minista Mai Kula da Tafiyar da Kasa, wato mai taimakawa shugaban kasa kan yaki da cin hanci.
  An taba ruwaito shi yana cewa: "Kowanne mutum yana da baiwar da Allah Ya yi masa. Allah Ya ba 'yan arewa kwarewa ne wajen shugabanci. Bayarabe wajen dogaro da kai da kuma kyawawan dabi'u. Igbo suna da baiwa wajen kasuwanci da kuma kere-kere. Allah Ya halicce mu daidai kuma kowa da baiwar da Ya yi masa."
Wasu sun yi amfani da wannan kalami nasa wajen bayyana damuwa game da yadda 'yan arewa suka mamaye fagen shugabancin kasar.
A shekarar 1957 gabanin Najeriya ta samu 'yancin kanta, marigayi Maitama Sule shi ne ya kewaya da Sarauniyar Ingila Elizabeth yayin da ta kai ziyara Kano yana yi wa jama'a bayaninta.
  A karshe, Ya rasu a watan yulin shekara ta 2017, ya bar 'ya'ya 10 - maza hudu, mata shida.
  Da fatan Allah yajikansa Amin

Abu Aiman
Social Media Yannmazan Jiya