KU TASHI TSAYE! KUYI HATTARA DUNIYA MAKARANTA (IYAYE)!!
A shekarun da suka gabata, talakawa masu karancin ilimin Addini da na Boko, masu tsananin Talauci sun rayu da iyalansu cikin hali na babu da tsabar wahala a rayuwa. Amma ya'ya'nsu sun sami damar yin karatut-tukan Boko da Addini, akasamu da yawa daga cikinsu sun zamo:
a. Likitoci (Doctors)
b. Injiniyoyi (Engineers)
c. Ya'n kimiyya da fasaha (Scientists)
d. Akowuntoci (Accountants)
e. Lawyoyi (Lawyers)
f. Masu Zane-zane (Architects)
g. Farfeso-shin ilimi (Professors). Wadan nan nakira su da group 'A'.
Ya'n group 'A' yaran da sukayi Gwagwar-mayar a karan Kansu bayan kammala Primary aji shida ko grade 12, suka zamo mahimman mutane a yanzu. Mafiyawan su sun:
👉 Je makaranta makaranta a kasa da kafafun su
👉 Je gona aikin kodago Dan abincin da zasu ci ko iyayen su.
👉 Debo Ruwa da Iccen konawa a kawunan su.
👉 Farawtar Namun daji.
👉 Wasu ayyukan kamar kasuwanci da kira da dai sauran su.
Ayanzu group 'A', wadan da suka zama IYAYE a yanzu, suka Samar da ya'n group 'B' ya'ya'nsu.
Wadan nan ya'n group 'B' yara ne masu;
✅ Gata gaba da baya
✅ Ana yimasu duk ayyukan dake cikin gida tin suna yan Nursery Har zuwa karatun gaba da sakandary
✅ An Sanya su a makarantun kudi mai tsada ko kuma an tura su kasashen waje domin suyi karatu
✅ Suna iya kallon movies tin daga safe Har Dare a Ranakun hutun mako
✅ Ana basu kulawa kamar yara jarirai ko Sarakuna ko ya'ya'n Sarakuna
✅ Basayin wani aikin gida komin kan-kantarsa
✅ Abinci da zasu ci sai an ajemasu shi a tebirin cin abinci
✅ Kwanon abincin ma sai andauke kuma an wanke a gidan
✅ Ana basu Manyan motoci da kaya masu tsada
✅ Ana basu kudin Sawa aljihunci ba tare da sun bukata ba
✅ Iyayen su ke taimakon su wajen yin Assignments
✅ Duk da haka ya'n kadan ne a cikinsu ke iya karatu da rubutu.
Ya'n group 'A' sun kula da iyayen su, da ya'ya'n su , Group 'B', ya'yan su suna nan suna gwagwarmaya su gaje su suna ya'n shekara 30!!
Amma kuma Abinda yazamo masu abu mai wahalar gaske sabo da sukayi a rayuwrsu komai sai antaimakesu kuma taimakon daga ya'n group 'A'. Don haka yakasance basa iya taimakon kansu da kansu, iyayensu ko kuma al'umarsu. Sun kyale iyayen suna horar da wasu yadda za'a sami duniya.
Me karatu a wane group kake?
❎ A rage ji-ji da kai da taimakon da baizama dole ba ga yara!
❎ Ka taimaki ya'yanka su tashi da wayansu da hikimarsu da kaifin kwakwalwarsu domin tunkarar kowane kalu-bale na rayuwar su lokacin da baka/ki
❎ Barsu su tinkari gaskiyar al'amari na rayuwa. Koya masu yadda zasu girma suna dogaro da Kansu!!
Koyar da ya'yan ka/ki ;
✅ Jin tsoron Allah
✅ Su girmama na gaba kada su raina kowa
✅ Koya masu jajircewa da dogaro da Kansu a rayuwa
Iyaye Ku hukunta ya'yanku in sunyi ba dai-dai ba domin su girma suna masu kare mutuncin kawunan su daku baki daya kuma su zamo masu anfani ga al'umarsu ba mararsa amfani ba ga kawunansu da Al'umarsu.
Allah ka shirya mana zuri'ah Amin..
Abu Aiman Danja
Duniya makaranta
15/01/2019.
No comments:
Post a Comment