Thursday, January 17, 2019

MATSALOLIN MASU GOGORIYON YIMA YARAN ISLAMIYYA WALIMA

Matsalolin Masu gogoriyon yima Yaran Islamiya walima

Daga Abu Sadiq Muhammad Bello

A gaskiya karatu yanzu ya zama abinda ya zama musamman a kasashen Hausa
Saboda son zuciya dake tattare da wasun mu dalibai da wasu daga cikin iyayen mu
Gaskiya na zabi wannan maudu'i ne saboda illa da hakan ke haifarwa yayi yawa

★Bari mu ga wasu daga cikin dalilan da yake sa wasu Malaman islamiyoyi ke RUSHING din Yara don ganin sunyi Masu walima

1-Azazzalawan iyaye da gaggawa wajen ganin yaransu sun sauke al-Qur'ani
2-Cire Yara daga duk islamiyar da ba a yima Yara walima duk shekara
3-San abin duniya daga wasu daga cikin Malaman
4-Rashin me da hankali a kan karatu

Wadannan wasu ne daga cikin dalilan da suka sa wasu islamiyoyin mu suke tunkuda Yara a karatu don ganin anyi sauka da wuri

★Yanzu za mu duba muga wasu daga cikin illolin da hakan ke haifar mana
1- a al'adar kasan Hausa kashi saba'in (70%) na Yaran da ake yima walima basu ci gaba da karatu musamman MAZA
To zaka ga yaro ya bar islamiya bayan sauka amma baze iya karntar da wani al-qur'ani ba
2-Zaka ga tun ana sauran wata daya ko biyu za a yankan ma yaro ayoyin da ze karanta ranar walima amma in ranar tazo ya hau mimbari se ka ga yana Jan ayar itama tana Jan shi
3-Hakan ya janyo mutane da dama basu San darajar karatu ba sun dauka makarantun da ake walima akai akai sunfi karatu
4-Kuma hakan ze janyo karancin kwararrun malaman da zasu karantar kuma su rike islamiyoyinmu a nan da wasu shekaru Masu zuwa

★Shawarwari ga iyaye, malamai da kuma mu dalibai akan wannan mas'alar

*IYAYE
1. Ya kamata ku Zama Masu taimakama malamai wajen kula da karatun Yara ta hanyar hada Masu extral timetable da zaku dinga duba Masu darrusan da ake Masu a Makaranta da kara Masu haske akan ababen d basu fahimta ba a Aji
2-Yakamata iyaye su tabbatar suna tura yaransu Makaranta a kan lokacin da hukumar Makaranta ta ajiye na zuwa Makaranta
3-Yakamata iyaye Sufi bada muhimmanci wajen lalubar wace Makaranta aka fi karantarwa ba Wai makarantar da akafi yima Yara walima ba
4-Siya ma Yara duk abinda suke bukata na karatun
5-Nuna ma Yara a shirye kuke Ku kashe Masu ko nawa ne matukar kuna da hali don ganin sunyi karatu
6-Bama malamai cikakken goyon baya don su karantar da Yara

*YARA
1-Muji tsoron Allah mu mai da hankali akan karatunmu
2-Mu dage da rokon Allah ya fahimtar damu ababen da ake koya mana
3-Mu girmama malamanmu

*MALAMAI
1-Kuji tsoron Allah Ku kawar da kai daga ababen da ake samu lokacin walima
2-Duk Wanda ya bude islamiya ya kamata ya zama yana da tsarin da yake tafiyar da karatunsa akai kuma karya bari wani yana juya akalar karantarwarsa
3-Ya dinga samun lokaci Koda sau daya ne a duk bayan wata uku yana gayyatar taro yana tattaunawa da iyayen yara don in akwai wata matsala anan yakamata atattaunata a samu mafita
4-Kada ayi ma yaro sauka har se ya sauke alqur'ani sauka na haqiqa ta yanda duk Inda aka bude masa ze karanta babu fargaba kuma babu gargada
Sannan ya taka matakai kamar haka
1. A kalla ya haddace arba'una Nawawi a bangaren hadisi
2. A bangaren tauhidi ha sauke usulussalaasa
3. A bangaren Tajwidi ya sauke kuma ya haddace tuhfatul atfaal
4. A bangaren fiqhu ace ya sauke kuma ya San akhdariy yadda ya kamata
5. A bangaren lugah ace ze iya rubuta wasika da larabcin
6. A bangaren sirah ace ya kammala Khulasatun nuurul yaqiin na farko
7. Sannan dole ya kasan ce yana da hadda karancin izu biyu

Wallahi duk makarantar da ta dauki wannan tsari kuma tasa shi a cikin tsarin makarantar kuma duka iyaye su rattaba hannu a wannan to a walimar su na farko za ayi mamakin irin hazikan Taliban da zasu have duk da dai nasan baza suyi yawa ba amma ai da haihuwar yuyuyu gwara daya kwakkwara
Kuma da ace irin wannan tsarin malamanmu suka yi amfani dashi tun muna islamiyah wallahi da yanzu mun wuce haka nesa ba kusa ba

Ina rokon Allah ya bama malamanmu ikon amfani da wannan shawarwari domin kannanmu Masu tasowa su wuce wannan mataki da muke kai amin.

Abu Aiman Danja
Social Media Strategists

📝Bincike/nazari da rubutawa📝
Abu-Sadiq Muhammad Bello #Al_Baiquniy

No comments:

Post a Comment