MAHAKURCI MAWADACI WATA RANA
1. An haifeka a mafi daukakar asibiti amma ni a gida aka haife ni amma gaba daya mun rayu.
2. kayi makarantar kudi ni ta gwamnati nayi amma mun hadu a jami'a / kwaleji daya.
3. ka kwanta a kan gado na kwana a tabarma amma gaba daya mun wayi gari, kowa ya nufi harkar sa.
4. ka saka kaya masu tsada ni kuma na saka masu arha amma duk mun rufe tsiraici.
5. ka ci jolof rice da farfesun kaji amma ni na sha koko da kosai amma dukanmu mun koshi, Alhamdulillah.
6. ka hau motarka mai tsada ni kuma na hau ta haya amma duk mun isa gurin da muka nufa.
7. wataqila kana karanta wannan rubutun daga wayar Sony xperia, q10, iphone6+ ni kuma ina wannan rubutun daga tsohuwar Nokia x2-01 amma dai wuri daya muka shiga; WhatsApp ko a Facebook.
Ya Ku masu karatu, rayuwa ba gasa ba ce akwai hanyoyi da yawa ta cimma buri.
1. Hanyoyi mabambanta kan kai mutane ga matsaya daya.
Don ka ga makwafcinka yana samun nasara kai ba yana nufin kai baka da nasara a rayuwa ba.
2. Farin ciki ba shine samun duk abinda rai ke buqata ba, Farin cikin shine samun wadatar zuciya da haquri da abinda Allah ya hore maka.
Manzon Allah (S.A.W) yace "yawan dukiya ba shine arziki ba, wadatar zuciya shine arziki"
Allah Ya kara mana wadatar zuci, Ameen.
Kada kayi gaba da mai son yin gaba dakai,idan ka ganshi kayi masa sallama. Kada ka damu da hassadan maihassada, barshi¬
muguntansa zata koma kansa. "Duk wanda ya ce duniya ita ce mafi mahimmanci a gare shi, To tabbas bakin cikin sa zai yawaita".
Kayi hakuri wurin barin sabon Allah, domin wani abun kanaso amma babu yadda zakayi,hakanan zaka barshi don jin tsoron azabar Allah. "Ba abin alfahari ba ne don ka yi rinjaye ga mai karfi, Abin alfahari shine ka yi adalci ga mai rauni".
Wanda ya fada maka magana mai zafi, kalma mai daci da 'kuna, mayar masa da tattausa mai taushi kamar ruwan sanyi. "ALLAHU ya bamu ikon ruko da gaskiya!!
MAFIFICIYAR ZUCIYA: ita ce zuciya sassauka, wacce batta rabuwa da gaskiya.
MAFIFICIN MUTANE: shine mutumin da bai manta dakai har abada. Saboda kaunar da yake yi maka Domin Allah ne.
MAFIFICIYAR RANA : ita ce ranar da tazo ta wuce baka aikata wani zunubi ba.
MAFIFICIYAR KYAUTA : ita ce addu'ar da wani yayi maka ba tare da saninka ba.
Allah nake roko ya yarda dani daku baki 'daya, ya yardar daku, ya yaye muku dukkan bakin-cikinku, ya saukaka muku dukkan lamarinku, kuma ya sanyaku acikin Ahalin gidajen Musulmi Aljannah Aameen.
Abu Aiman Danja
Social Media Strategists.
No comments:
Post a Comment