Thursday, January 10, 2019

"AURE KO MAKARANTA" SAKIN NA HANNU KAMUN NA GUJE!!


 Mafiyawa YAN'MATA da samari a KASAR Hausa a wan nan Zamani Suna tsintar kawunansu cikin wani yanayi mai Hadarin gaske Wanda kai mafi yawa-yawan yan'mata ga yin da nasani!!

Yayin da Saurayi yaje neman auren mace 'yar shekara 18+ mafi yawa daga cikin su haka za su fada maka.

Idan kuma macen ta nuna tana da ra'ayin auren, sai a bata shawara, da cewa: "karatun nan shi ne gatanki, idan ba kiyi ba za ki zama 'ci ma zaune' don haka kada ki yarda, zaki zauna komai sai kin jira mijinki ya miki". Ko ace mata " idan mijinki ya sake ki ko kuma mijinki ya mutu, za ki sami aikin gwamnati, ki dogara da kanki, amma idan ba ki yi karatu ba za ki zama mai bara da maula akan titi"! Data nan sai ta kafe lallai karatu zatayi shi kuma saurayi ya tafi.

Yayin da ta gama karatun, lokacin ta kai shekara 23 ko 24. Lokacin sai burinta ya karu, saboda tana jin cewa, ta kai wani babban matsayi, ta sami shedar DIPLOMA, N. C. E., ko DEGREE. Sai irin mijin da ta tsarawa kanta za ta aure. Samarin da a baya take kulawa, yanzu likafa ta ci gaba,tana ganin tafi Martin su ko kuma ta raina su. Samari suyi ta zuwa, amma ta tsaya ruwan ido, sai mai kaza da kaza (abin duniya) saboda sai ta zaba. Haka za tai tayi har takai shekara 28 zuwa 30 ko 33. Lokacin samarin sun fara tafiya suna barinta, saboda shekarunta sunyi yawa.

Ana cikin haka, sai kuma bukatar auren ta kama ta sosai, ba zato ba tsammani. Saboda lokacin sa'aninta sun hayayyafa, sunyi zuriyya. Ita ce shiga malamai dan neman addu'ar samun miji. Da zuwa makarantun Islamiyyu dan sa yara dalibai su taya ta da addu'a Allah ya kawo mata miji, ta hanyar raba musu biskit da alewa.

Haka abubuwa za suyi ta kasancewa, idan Allah ya taimake ta sai kaga ta auri Tsoho sa'an mahaifinta, ba dan shi take so ba, a'a, sai dan ta rasa wanda take so. Wata kan haka za tai ta zama, har shekara 40 ko 45- Lokacin ta zama ta al'umma, sai dai aikin office (idan ta sami aikin kenan). Za tayi ta samun promotion a wajen aiki, ga kudin ta samu amma ba kwanciyar hankali!!!

Allah ya kiyaye (ba fata ake ba), idan ba ta sami aikin ba, ko kuma ta samu, amma babu miji, ga shi kulkun sha'awar d'a namiji tana damun ta. Wata a nan sai ta kauce hanya, ta fara bin 'yan samari tana basu kudi suna amfani da ita, dan ta sami gamsuwar sh'awarta, wato ta zama (sugar mummy).  Wata kuma ta koma harkar neman mata 'yan uwanta (lesbianism), wata kuma ta zama karuwa mai lasisi, ta hanyar bin ma'aikata, abokan aikinta.  Idan kuma Allah ya so, sai ta zamo me yawan ibada, azumi da sallah. Wan nan shine sakin Na hannu kamun Na guje.

 Hattara mata a yi tunani sosai, aure baya hana karatu, haka zalika, karatu ma baya hana aure. Abi Allah a zauna lafiya.

Abu Airman Danja
Social Media Fadakarwa.

2 comments: