WATA SABUWA!!!
NAZARI AKAN TASHAR TALBIJIN TA AREWA-24
Daga Kabir Bagudu Bichi
Da
Iliyasu Muhd Wada
Ina masu kallon wannan tasha ta Arewa24, ina mai maku sallama irin ta
addinin muslunci;
Assalamu alaikum.
A matsayina na Musulmi, kuma ‘dan Nigeria kuma ‘dan Arewa, na zurfafa wani binci ke, (Domin ni mai sha’awar
bincike ne akan duk abinda nake ko nake
so) wanda nake ganin yana da matukar
muhimmancin dukkanin ma’abota kallon wannan tasha su amfana da sakamakon wannan bincike nawa. Amma yana da kyau akan duk wanda ya karanta wannan rubutu nawa kada ya yanke mun hukunci har sai ya karanta rubutun tun daga farko har karshensa. Na biyu kuma duk abinda na rubuta wanda mai karatu bai gamsu da shi ba, to kafin ya yanke mun hukunci ina rokon sa da yayi bincike, ko ya tambayi masana da yake
ganin suna binciken ababen dake faruwa
a duniyar yanzu, ko ma yayi amfani da kafar bincike ta internet domin binciken wannan jawabi nawa. Da fatar Allah ya shige mana gaba adukkanin ababen da muka sani a fili, da kuma wadanda suke a ‘boye.
Da farko ni mai sha’awar kallon wannan tasha ne ta Arewa24, sakamakon suna gudanar da shirye-shiryensu da harshen Hausa, kuma ni bahaushe ne. Haka zalika yanayin fitar da hotonsu acikin quality mai kyau, ya taimaka a wajen samun sha’awata a gidan TVn, sai kuma wasu shirye-shiryen su.
To amma ababe daywa suna daure mun kai, ganin yadda ake kashewa gidan TV kudi masu yawa tare da daukar ma’aikata masu yawa, da gudanar da shirye-shirye masu yawa wadanda ke bukatar kudi da yawa kamin a hada su.
Kuma duk ace gidan TV yana yada shirye- shiryensa kyauta, kuma babu wasu kampanoni da ke daukar nauyin gidan TV (sponsors/Adverts) ga zun zurutun kudin albashi da ake fitarwa a kowane wata. Wannan shine dalili na farko da ya jawo hankali na, na gudanar da wani gajeren binciki akan:
-Su waye ke daukar nauyin wannan gidan
TV me tsada haka?
- Ko anan gaba gidan TVzai koma na kudi
ne??
- Ko akwai wasu manufofi da sune
dalilin kafa wannan gidan Tv??
Ganin wasu shirye-shirye da suka ci karo
da al’adun Hausawa da Addininsu, kamar
shirin H Hip Hop, ko meye manufar ire-
iren wadannan shirye shirye??
Wannan
sune kawai dalilina na gudanar da wannan bincike da nayi, kuma na samu bayanai da suka gamsar dani, na
wa dannan tambayoyi.
1. Mai karatu SHIN KO KA SAN CEWA Arewa24 gidan tv America ne, Karkashin kulawar Federal bureau of Investigation Washington?
2. Mai karatu SHIN KO KA SAN CEWA
wannan gida Tv an ware masa
zunzurutun kudi har Dala Miliyan 60 ($
60m)?
3. Mai karatu SHIN KO KA SAN CEWA An gina wannan gidan Tv domin rikicin da yake faruwa na BOKO HARAM? A tunanin su wannan gidan Tv zai taimaka wajen dauke hankalin samari daga zurfafa ga Ilimin Addinin Islama wanda suke tunanin kan iya taimakawa wajen kirkiro kungiyoyi tare da mara masu baya iren-iren BOKO HARAM. Ta hanyar kirkiro shirye-shirye irinsu Hip Hop wanda ake tunanin zai yi kokarin da kashe zafin kan addini daga matasa, Kamar shirin zauren malamai; wanda akoda yaushe yana Magana ne akan JIHADI, ta hanyar tara wasu malamai da basu yi fice a wannan yanki namu ba akan karantarwar addini.
Amma suke kokarin bayar da ma’anar JIHADI a muslunci da kashe-kashen sa.
4. Mai karatu SHIN KO KA SAN CEWA shirin DADIN KOWA babbar manufar shirin ita ce; daga karshe a nuna yadda malaman
Addini ke komawa ‘yan boko haram, tare da amfani da matasa.
5. Mai karatu SHIN KO KA SAN CEWA yanad aya daga cikin manufar kafa wannan gidan Tv, daidaita matsayin Maza da Mata acikin al’ummar Arewa, ta hanyar amfani
da shirye-shirye iri daban daban
6. Mai
karatu SHIN KO KA SAN CEWA
dukkanin shirye-shiryen wannan gidan Tv
ana tace su ne kadai anan Nigeria (Shooting and Editing) Amma sai ankai su America ake sakasu a satellite (Airing)
7. Mai karatu SHIN KO KA SAN CEWA wasu
manufofin kafa wannan gidan Tv, ko
ma’aikatan wannan gidan bazasu san su
ba a yanzu (Kasan cewar muna fama da rashin aikin yi sosai a wannan kasa, shi ke
sa ba wani cikakken bin cike da mutanen
zasu yi a yanzu, su dai bukatarsu su samu
a ikin yi) Domin turawa sun yi nisa wajen
boye manufarsu, sai tafiya tayi nisa sosai
zasu rika fitowa a fili.
8. Mai karatu SHIN KO KA SAN CEWA Duk
shirye-shiryen da kake gani a yanzu an
a shirya su ne domin jawo hankalin jama’a
ga wannan gidan Tv, amma cikakkiyar
manufar sai nan gaba sosai zata yi tasiri!!
Mai karatu ba ina kokarin goyon bayan kafa kungiyoyi irinsu boko haram bane,
sai dai ina tsoron, a tafi “gyaran gira a
tsone idanuwa” Sakamakon lalacewar
tarbiyar da wasu daga cikin shirye-
shiryen su zai iya haifarwa, musammam H
Hip Hop, wanda tun a yanzu ya fara daukar hankalin matasa da ‘ya’yanmu
matuka. Mai karatu ina tsoron ire-iren
wadannan
gidajen Tv da America ke kafawa domin
bincike na, na gano wasu da aka gina a
wasu kasashen Africa dana labarawa wanda America tayi, na kuma samu
bayanai na tasirinsu a wadannan
kasashe, wajen kokarin sauya masu
al’adu. Mai Karatu manufar wannan
rubutu nawa
shine, muyi taka tsan-tsan da wannan gidan Tv. Mu san ire-iren shirye-shiryen da
zamu bar ‘yan’yanmu suna kallo a
wannan gidan Tv. Daga karshe mai
karatu, ni da nake
wannan rubutu dalibi ne a Jami’a bana da
wata manufa ta kushe wannan gidan Tv, domin kona kushe shi bani da wani da
zan gabatar maka a madadinsa, face nayi
ne kawai domin fadakar da ‘yan uwa
musulmi. Idan kuma akwai akasin haka
to Allah na gani kuma zai saka masu.
Amma dai kai kanka mai karatu kayi naka binciken, domin na tabbatar da
cewa wannan rubutu nawa ba zai jima
akan internet ba, zasu goge shi Domin
Karin bayani mai karatu ya ziyarci
wadannan �pages din;�
http://www.ibtimes.com/arewa24us-launches-
nigerian-tv
http://www.premiumtimesng.com/tag/
arewa24
http://newsrescue.com/nwo-landed-nigeria-us-
sponsor
Forwarded as received