KASANCE TARE DA NI A WAN NAN SAFIN DOMIN FADAKARWA, TINA TARWA, ILIMANTARWA, NISHADANTARWA, DUNIYA MAKARANTA, KIMIYYA DA FASAHA, SABIN DABARUN BUNKASA SANA'O'INKU A ZAMANANCE, KIWON LAFIYA, TARIHI, DA DAI SAURANSU.. KUBIYONI ALLAH YABAMU SA'AH AMIN
Wednesday, December 26, 2018
BUHARI ZAI FARA YAKIN NEMAN ZABE A AKWA IBONBON
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari zai kaddamar da yakin neman zabensa wa’adi na biyu a ranar Juma’a mai zuwa a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
Sanata Ita Enang da ke taimaka wa Buhari kan al’amuran da suka shafi Majalisar Tarayya ya sanar da haka a yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin a Uyo.
Enang ya ce, shugaba Buhari zai kasance a jihar tare da shugaban Jam’iyyar APC mai mulki, Adam Oshiomhole da sauran jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar don kaddamar da yakin neman zaben a hukumance.
Sanatan ya ce, jam’iyyar APC ta nemi izinin amfani da katafaren filin wasan kasa da kasa na Akpabio kuma tuni gwamnatin jihar ta amince a cewarsa.
Kamfanin Dillancin Labaran kasar, NAN ta ce, a ranar 23 ga watan Disamba, gwamnatin jihar ta ce, ba za ta bayar da filin don gudanar da yakin neman zaben ba saboda wasannin firimiyar kasar.
Abu Aiman Danja
Social Media Star
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment