A RANAN LAHADI 30/12/2018. TSAFFIN DALIBAN KIMIYYA DA FASAHA WADAN DA SUKA KAMMALA KARATU A SHEKARAR 2013 SUKA DAGA DEPARTMENT OF CHEMISTRY BAYERO UNIVERSITY, KANO ( BUK) SUKA GUDANAR DA TARON SABUNTA ZUMUNTA A TSAKANINSU TARE DA GAYYATO WASU DAGA CIKIN MALAN SU
ANDAI FARA WAN NAN TARO DA AKAYIWA SUNA DA HARSHEN TURANCI REUNION OF CHEMISTRY CLASS OF 2013 DA KIMANIN 2:30PM, YAYIN DA MAFI YAWA DAGA CIKIN TSAFFIN DALIBAN KE CIGABA DA HALARTAR TARON CIKIN FARIN CIKI DA ANNASHWA. DUKDA KASANTUWAR TARON SHINE KARO NA FARKO DA SUKA TABA SHIRYAWA.
DAYA DAGA CIKIN MANYAN BAKIN DA SUKA HALARCI TARON DR. I.T. SURAJ LEVEL COORDINATOR NA YA'N PURE CHEMISTRY A LOKACIN SUNA UNDERGRADUATE, YA NUNA FARIN CIKINSHI DA JIN DADINSHI GAME DA KOKARIN DA TSAFFIN DALIBAN SUKAYI DOMIN FARA IRIN WAN NAN TARO DA WURI, YAKARA DA CEWA A LOKACIN DA SUKAYI NASU YA ZAMTO BAYAN SHEKARA ASHIRIN DA KAMMALA KARATUSU SANNAN SUKA SHIRYA WA KANSU IRIN WAN NAN TARON. KUMA YA YABAWA TSAFFIN DALIBAN DA CEWA KUN ZAMO NAKWARAI KUMA MUNA ALFAHARI DAKU DOMIN KUN KASANCE MASU KISHIN KANKU DA COMPETITION A TSAKANINKU WANDA HAKAN YA ANFANEKU DON HAKA KUKA KAMMALA KARATUNKU LAFIYA DAGA KARSHE YAYI ADDU'AH DA FATAN ALKHAIRI GA WADAN DA SUKA ZO DA WADAN DA BASU SAMI HALARTA BA.
DAGA SASHIN TSAFFIN DALIBAN KUWA SUN NUNA MURNA DA FARIN CIKI YAYIN DA SUKA HADU A DAKIN TARON, ANCI ABINCI TARE KUMA ANYI HOTUNA DUK DA WASU SUNZO NE DAGA BAYAN AN KAMMALA TARON.
DAYAWA DAGA CIKIN TSAFFIN DALIBAN SUN FARA AIKI A WASU MADAFIN IKO NA KASAN NAN WASU SUNA BANGAREN KOYARWA, WASU SUNA BANGAREN TSARO, WASU KUMA SUNA AIKI DA NGOS, DA DAI SAURANSU. TARON WANDA SHINE NA FARKO HAKIKA YA JA HANKALIN MAFI YAWAN YAN AJIN.
No comments:
Post a Comment