KASANCE TARE DA NI A WAN NAN SAFIN DOMIN FADAKARWA, TINA TARWA, ILIMANTARWA, NISHADANTARWA, DUNIYA MAKARANTA, KIMIYYA DA FASAHA, SABIN DABARUN BUNKASA SANA'O'INKU A ZAMANANCE, KIWON LAFIYA, TARIHI, DA DAI SAURANSU.. KUBIYONI ALLAH YABAMU SA'AH AMIN
Wednesday, December 26, 2018
Buhari Shugaba ne mai Amana – Shugaban kungiyar Qadiriyya
Shugaban kungiyar Qadiriyya a Afrika, Sheikh Qaribullah Nasir-Kabara ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai amana.
Sheikh Kabara ya bayyana hakan ne a lokacin bikin maulidin da aka gudanar a Kano - Ya nuna goyon baya ga shugaban kasa a kokarinsa na daidaita amuran Najeriya akan tafarkin ci gaba Shugaban kungiyar Qadiriyya a Afrika, Sheikh Qaribullah Nasir-Kabara ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mai amana da sauraron matsalolin jama’a. Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne a lokacin bikin maulidin da aka gudanar a Kano. Nasiru-Kabara yace shugaba Buhari na da son ci gaban kasar a zuciyarsa sannan kuma ya kamata duk masu son ci gaban Najeriya su mara masa baya. Buhari shugaba ne mai amana – Shugaban kungiyar Qadiriyya Source: Twitter Ya tuna cewa a lokacin ziyarar da shugabannin suka kaiwa shugaban kasar a fadarsa a kwanakin baya yace anyi gaggawar magance wasu matsaloli da suka gabatarwa gwamnati Read more: https://hausa.legit.ng/1211429-buhari-shugaba-ne-mai-amana-shugaban-kungiyar-qadiriyya.html
Abu Aiman Danja
Social Media News
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment