Sunday, December 30, 2018

RIKI-TACCAEN TSOHO!

RIKITACCEN TSOHO!

Wani Saurayi yana tafiya a hanyarsa ta zuwa Rumfar mai abici, sai ya hangi wani Tsoho sai sharbar kukansa yake ba kakkautawa!, sai tausayin wannan tsoho yakamashi. Sai ya nufi wurin tsohon: Baba lafiya kake irin wannan kuka haka? Sai wannan tsoho yece:yaro ina da mata yar kimanin shekara(22)a gida. Kullum da safe sai ta yimin tausa kuma ta soya min kosai, ta yimin koko, ta kuma dafamin shayi mai dadi. Sai saurayin yace to me yasa kake kuka?.

Tsohon yace:Da rana kuma tayimin miyar Alayyahu da tuwon shikafa mai dadi ta kuma hadamini zobo mai sanyi,ta kuma tsaftace gidan. Bayan ta gama, sai tazauna kusa dani ta kunna mana talabijan muyi kallo cikin jin dadi har yamma. 

Sai Saurayi yace baba har yanzu baka fadamin abinda yasa ka ke kuka ba!. Sai tsoho yace: da Daddare kuma tayimin alkubus da romon kaza'ta, kuma ta matse lemo ta kawo min, naci na sha cikin annashuwa. sai wannan saurayi yace to duk da wannan abu da take maka me kuma yasaka kuka baba? Ko ta mutu ne?. Sai tsoho yace: yaro kar ka karayin maganar mutuwa kawai dai Hanyar gidan ne na manta

SHIN KO KASAN CEWA ISTIGFARI YANA KAWO ARZIKI??
➡WALLAHI IDAN HAR KA LAZIMCI YIN ISTIGFARI ZAKAGA ABIN MAMAKI DOMIN NI NA JARABA NAGANI.
KA LAZIMCI FADIN↙⬇
 "ASTAGFIRULLAHI WA ATUBU ILAIHI"
WLH KOMAI DAMUWARKA ALLAH ZAI YAYEMAKA. ZAKAGA BUDI.
JARRABA KANA ME IMANI DA ALLAH...

Abu Aiman
Social Media Fadakarwa

1 comment: