Wednesday, December 26, 2018

WAYAR ANDROID AKAN KUDI 500 TA FARKO A AFRICA


Wayar Android Akan Kudi N500 Ta Farko A Africa

A ranar 30 ga watan da Nubamban wannan shekara ta 2018 kamfanin Beep Tool ya kaddamar da wata wayar hannu kirar android domin talakawa masu karamin karfi akan kudi N500 kacal a birnin tarayya Abuja.

Idan mutum yana samun N15,000 a wata to ya yiwa Allah da ma'aiki ya hakura da siyan wannan wayar domin an yita ne domin talakawa zalla a cewar kamfanin.

Sai dai wannan wayar na dauke da tarin tsarabe-tsaraben dokoki da sharuda wadanda zamu iya cewa 'kowa yaci ladan kuturu to fa tilas ne yayi masa aski' Inji 'yan magana.

Daga cikin sharuda da wannan waya ke dashi sun hada da:
1. Akwai Garanti da Idan ta samu matsala zasu sake ko su gyara maka.
 a. Idan ta samu matsala ka gaggauta sanar musu cikin lokaci.
b. Ida ka sanar da samun matsalar wayarka za'a karba sannan ka dawo cikin sati daya domin karbarta idan ta gyaru ko kuma an canja maka, idan baka sanar da wuri ba har aka samu tsawon lokaci to kaine zaka dauki asara.
2. Wayar tana sanye da tsarin da kamfanin yana ganin duk wata zirga-zirgar ta da kuma inda take.
3. Idan wayar ta samu damage kamar fashewa ko aka sace ko kuma 'Yan fashi to kai zaka dauki asara bisa wadannan sharadan dake kasa:
a. Idan ka rasa wayarka sata/fashi to abu na farko kayi gaggawar sanar da police station mafi kusa da abin ya faru sannan ka sanarwa kamfanin su kuma zasu bibiyi inda take, kuma duk aikin wannan kaine zaka biya.
b. Idan aka gagara gano wayar to zaka biya kamfanin N27,375.
c. Kana da damar yi mata gyare-gyare kamar rufeta da riga screen guard da sauransu.
d. Idan wayar ta samu matsala ta dalilin wani sakacinka to ba'a yarda a canja wani abu nata ba har sai ka nemi iznin kamfanin.
4. Wayar tana bukatar Network domin amfani da ita, saboda haka zaka dinga siyan Data (MB) duk wata mafi karanci 1GB kuma a gun kamfanin zaka dinga siya akan N800.
a. Idan kaki biyan kudin data din to kamfanin zai rufe wayar daga aiki.
5. Kamfanin zai dinga saka talluka na SMS, hoto, video da kuma a social media akan wayar har tsawon watanni 24.
6. Kamfanin zai dinga sanya Application da cirewa daga kan wayar a duk sanda ya bukata.
7. Kamfanin zai hanaka aiwatar da duk wani abu da bai dace ba da wayar.
8. Bayan watanni 24 wayar ta zama zasu cire dukkan wani abu nasu akai.
9. Duk wanda yaje samun kudi N500 to bashi da damar mallakar wannan wayar.

Wannan fa shine wai adashin gata.

Domin karin bayani ko siyan taka wayar sai ka shiga shafin kamfanin https://www.oyi.beeptool.com

Allah ya bada sa'a.

Abu Aiman Danja
Social Media Strategist

No comments:

Post a Comment