Wednesday, December 26, 2018

ABIND KUKE NAMA GAME DA SHIRIN P-YES YA SAMU


ABINDA KUKE NEMAN SANI GAME DA SHIRIN P-YES

P-Yes ko Presidential Youth Empowerment Scheme shiri ne da ofishin Shugaban Kasa ya kirkiro karkashin Jagorancin Mai baiwa shugaban Kasa Shawara na Musamman akan Harkokokin Matasa da Dalibai.

ABIN BURGEWA GA SHIRIN

Wani abin burgewa da Shirin shine yadda aka zabo kananan Sana'oi da al'umma ke bukata a ko wace rana, a ko wace unguwa, Ko wane Gari, Ko wane Kauye.

Sana'oi ne da Matashi zai iya yi ko ina, a ko wane lokaci. Dare ko Rana, Sanyi ko Zafi, Rani ko Damina

Sana'oin Basu bukatar Kama shago. Kawai matashi na bukatar dan Inda zai raba ne, kamar gefen titi, ko runfar kasuwa, koma cikin gida don gudanar da sana'ar shi.

MINENE MANUFAR SHIRIN

Manufar shirin P-Yes shine;

1) Samarwa Matasa ayyukan yi don dogaro da kawunansu

2) Rage Yawan aikata miyagun Laifuffuka da Shaye Shayen Kwayoyi tsakanin Matasa ta hanyar samar masu da ayyukan yi.

3) Rage fatara da talauci da zaman kashe wando tsakanin Matasa.

4) Habaka tattalin arzikin Nigeria ta hanyar baiwa Matasa damar bada gudummuwar su

5) Kirkiro da karin yawan Kanana da Matsakaitan Sana'oin da zasu samar da ayyukan yi da karin kudade a hannun matasa.

6) Dora matasa bisa turbar da zasu iya daukar nauyin kawunansu.

7) Ba matasa damar bada gudummuwa ga kokarin kawo ci gaban kansu da al'umma baki daya.

8) Habaka noma, Kiwo da Kananan Sana'oi don samar da arziki Mai Yalwa tsakanin Matasa.

MUTANE NAWA ZASU AMFANA DA SHIRIN

Shirin P-Yes an kirkiro shi don samarwa Matasa 774,000 ayyukan yi a fadin kanan hukumomi 774 dake fadin Nigeria.

SUWA SUKA CHANCHANCI SHIGA SHIRIN

Dukkan matasa sun chanchanci shiga shirin.

1) Matasan da Suka Yi karatu mai zurfi

2) Matasan da basuyi karatu mai zurfi ba

3) Matasan da basu yi karatun boko ba kwata kwata.

#BABBAN_ABINDA_AKE_BUKATA_SHINE_MATASHI_YA_ZAMA_ZAI_IYA_KOYON_ABINDA_AKE_SON_KOYA_MASHI

WANE SANA'OI NE CIKIN SHIRIN

Shirin ya kunshi sana'oi guda 21.

1) Noman Rani da
2) Damina
3) Kiwon Kaji
4) Kiwon Kifi
5) Sarrafa amfanin Gona (Casar Shinkafa)
6) Girke Girke da Dafe Dafe
7) Saida Abinci
8) Aski
9) Gyaran Gashi Na mata
10) Kwalliya
11) Dinki
12) Saka
13) Ado da Kwalliya
14) Daukar Hoto
15) Wankin Mota
16) Fachi
17) Welder
18) Gyaran Mota
19) Gyaran Wayar Salula
20) Gyaran Computer
21) Aikin Jinya da Aikin Likita

KA'IDOJIN SHIGA SHIRIN

MUHIMMIN ABU SHINE Kafin matashi ya shiga shirin yana bukatar samun wani Matashin da zasu hada hannu (Dan goyo).

A Shirin dole matashi yana bukatar wani matashin a matsayin wanda zai amfana na 2 (Second Level Beneficiary).

Sauran Ka'idon da Ya zana wajibi Matashi ya cika;

1) Lambar Waya
2) National ID Card/Voters Card, International Passport
3) Wanda Zaka Goya
4) Cike Takardar shaidar wanda zai tsaya maka/ki (Grantor) (Shugaban Addini, Ko Hakimin Gargajiya)
5) Sa Hannun Shugaban Karamar Hukuna
6) Cike Takardar bukatar shiga Shirin
7) Dole Matashi ya zama za'a iya Koya mashi, kuma ya koya
8) Dole Matashi ya zama mai kyakkyawar Dabi'a
9) Matashi Zai iya Kasancewa tun daga Dan Shekara 18 - 40
10) Dole Matashi ya Zama Dan Nigeria
11) Dole Matashi ya kasance yana iya koyar da wani irin wannan Sana'ar bayan shima ya koya.

INA MAI BUKATA ZAI IYA CIKE TAKARDAR BUKATAR SHIGA SHIRIN

Za'a iya cika takardar neman shiga shirin a shafin yanar Gizo da aka tanada don wannan. A www.p-yes.org.ng

Ko kuma a cike takardar bukatar da za'a iya samu a offishin mai baiwa shugaban kasa shawara akan Cigaban Dalibai da Matasa dake Sakatariyar Gwamnatin Tarayya, Abuja.

ME MATASHI ZAI AMFANA DASHI A CIKIN SHIRIN

Shirin zai baiwa matashi horo na musamman akan sana'oin da suka zaba, suka kuma samu nasarar tantacewa don amfana.

A karshen horaswa, za'a baiwa matashin Kayan yin Sana'ar da ya koya bisa sharadin da za'a gindaya mashi.

Shirin ba zai baiwa matasan da aka horas kudi ba. Saidai kayan yin sana'ar da suka koya

Shirin na bukatar dole matashi ya koyar da wani matashi a area da yake irin sana'ar da ya koya a cikin tsawon shekara 1.

Allah ya bada Sa'a.

Don karin bayani ana ita tuntuba ta.

Abu Aiman Danja
Social Media Strategies.
Ziyarci shafin mu a www.aimanakowadanja.com.ng

No comments:

Post a Comment