Sunday, December 30, 2018

ILLAR FUSHI KO RASHIN HAKURI


Fushi  Ko Rashin Hakuri a Rayuwa Tamkar tabin hankali ne Karshen shi kuma Nadama ne, Inji *Aliyu Bin AbiTalib (R.A)* Ka lura Duk wanda fushi ya shafe shi yakan fidda shi daga dabi'a irin ta mutane,FUSHI shine tarkon abin da shaidan yafi amfani da shi wajen halaka dan Adam. Inji Ibnul Qayyim.Ka lura in mutum yana cikin fushi to yakan iya aikata komai a fusace Sannan Ba'a gane mutum me hakuri sai a lokacin FUSHI. Maganin fushi  manzan Allah (s a w) yace idan kai fushi idan kana tsaye ne kazauna idan kana zaune ne ka kwanta ko kuma kabar wurin da aka saka kai fushin. Ya Allah kasa mu iya hadiye fushin mu, mu iya yafe ma "yan uwan mu dan mutsira ranar gobe kiyama.ALLAH  ka jikan iyayenmu da yanuwanmu,da abokan mu, ya Allah kasa mufi Martin zuciyar mu yayin da fushi ko basin Rai! Ameen.

Abu Aiman
Social Media Fadakarwa.

No comments:

Post a Comment