Wednesday, December 26, 2018

ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WAJEN YIN TSAYUWAR DARE.

*ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WAJAN YIN TSAYUWAR DARE*

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa "Na hore ku da tsayuwar dare domin al'ada ce ta managarta da su ka zo gabaninku, kuma tana kusantarwa zuwa ubangiji, tana kuma kankare zunubai" Tirmizi.

An tambayi Hasanul Basary cewa : (Me ya sa masu tsayuwar dare su ka fi kowa kyan fuska, sai ya ce: saboda sun kadaita da Ubangijinsu sai ya tufatar da su daga haskensa)

ٍSaidai akwai abubuwa da suke taimakawa akan haka ga wasu daga ciki :

1. Baccin rana : Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : " ku yi baccin rana domin shaidanu ba sa baccin rana" Hasanul Basary ya wuce wasu mutane a kasuwa, sai ya ce wadannan ba za su yi bacci ba, sai aka ce masa E, sai ya ce ina ganin darensu ba zai yi kyau ba" ma'ana ba za su iya tsayuwar dare ba.

2. Yin bacci da wuri , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya karhanta bacci kafin sallar isha da kuma yin hira bayanta, kuma dalilin da ya sa ya karhanta hin hira bayanta saboda hakan zai iya hana mutum tsayuwar dare.

3. Aikata ladubban bacci yayin kwanciya, ta yadda zai karanta abin da ya zo a cikin sunna na ladubban bacci.

4. Umartar wani ya tashe shi kamar matarsa ko wanda suke tare.

5. Rashin cika ciki da abinci.

6. Nisantar yin aiki mai wahala da rana.

7. Nisantar abin da zai kawo maka fargaba a cikin zuciya, ta hanyar rage burirrika da tunanin abin da ya wuce.

8. Nisantar zunubai, Fudhail bn Iyadh yana cewa : "idan ka ga ba ka iya tsayuwar dare, to ka tabbatar zunubanka sun yi yawa.

*Amsawa:✍🏻*

*Dr. Jamilu Yusif Zarewa.*
20/03/2013

Daga
*ZAUREN FIQHUS SUNNAH* / *MImBARIN Malamai*

Abu Aiman Danja
Duniya Makaranta

No comments:

Post a Comment