ZUWA GA MASU KALLON HOTUNA DA VIDEOS NA BATSA
1- shin kun san abubuwan da kuke kallo yana daga cikin manyan laifuka (kaba'ir ).
2- shin kun san abinda kuke kallo yana gadar da kaskanci da kuma rauni ta kowane bangare.
3- shin kun san abinda kuke kallo yana kawo raunin idanu da kwakwalwa, da yawan mantuwa, abu kankani sai kamanta.
4- shin kun san wannan kallon yana sa mutum ya fadi a idon Allah.
5- shin kun san wannan kallon yana hana mutum samun ilimi ko mantashi.
6- shin kun san wannan kallon yana hanaka /ki samun jin dadin rayuwar aure mai inganci da mijinki ko matarka, kuma duk da kuna son juna.
7- shin kun san cewa zaku iya mutuwa a cikin wannan yanayin ( mummunar cikawa).
8- shin kun san jikinku zai gaya muku ko badade ko bajima in baku tuba ba.
9- shin kun san duk abinda kuka yada kuna da zunubi, inma yai sanadiyyar lalacewar wani kuna da zunubin koda kuna kwance akabari har izuwa kiyama.
10- shin kun san cewa duk wanda yabar wani abu domin Allah, Allah zai musanya masa da abinda yafishi alkhairi.
11- shin kun san cewa Allah yana farin ciki sosai da tuban bawansa.
12- shin kun san cewa Allah zai wadataku da falalarsa idan kuka kame kawunanku gada haramun.
13- shin kun cewa sha'awar yan mintina ta haramun tana dai dai da azabar shekaru.
YAN UWA MUSULMI KU TAIMAKI YAN UWAMMU WAJEN ISAR MUSU DA SAKON NAN KO ALLAH ZAI SHIRYASU TA DALILINKU KUSAMU LADANSU .
Abu Woman
Social Media Fadakarwa
No comments:
Post a Comment