KASANCE TARE DA NI A WAN NAN SAFIN DOMIN FADAKARWA, TINA TARWA, ILIMANTARWA, NISHADANTARWA, DUNIYA MAKARANTA, KIMIYYA DA FASAHA, SABIN DABARUN BUNKASA SANA'O'INKU A ZAMANANCE, KIWON LAFIYA, TARIHI, DA DAI SAURANSU.. KUBIYONI ALLAH YABAMU SA'AH AMIN
Tuesday, December 25, 2018
YADDA ZAKA NEMI SCHOLARSHIP TA WAYAR SALULA
[Fasahar Zamani] Yadda Zaka Nemi Scholarships Ta Wayar Salula
Kamar yadda muka sha fada duniya a yanzu anyi cigaba fiye da yadda muke tsammani domin ko yaushe kara zuwa ake da sabbin fasahohi iri-iri.
Wato Bahaushe yayi gaskiya da yace “Indaranka Ka Sha Kallo”
Yadda Tsarin Yake:
Tsarine da zai baiwa dalibi dama ya shigar da bayanansa cewa shine wane dan aji kaza a makaranta kaza a bangare kaza, shikenan cikin ‘yan dakiku zai kawo maka jerin scholarships a wannan yanki namu na Africa abinda ya rage maka kawai sai nema.
Tsarin yana lura da yanki da kuma matakin karatun mutum kamar wanda ya gama Sakandire ko mai digiri da mai masters d.s sannan ya baiwa mutum dai-dai dashi a irin salon nan da malam Dan Hausa ke cewa “Dai-dai ruwa dai-dai tsaki”.
Yaya Ake Yin Tsarin?:
Ka shiga Play Store a wayarka sai kayi searching application mai suna “SomaApp” shikenan kayi installing dinsa a wayarka, kana shigar da bayanan ka, shi kuma Malam SomaApp zai lalubo maka jerin scholarships da suka dace da kai.
Game da SomaApp:
Wani kamfani mai suna SomaApp Technologies Company Limited dake kasar Tanzania ne suka kirkire shi.
Wani abin mamaki shine yadda turawa suka dinga korafin cewa don me su ba’a saka nasu yankin ba?
Wato dai wannan abune da ‘yan Africa sukayi wanda suka kere turawa kuma a fasahar zamani.
Izuwa yanzu akwai mutane sama da dubu goma 10,000 dake amfani da wannan application din a duniya.
SomaApp dai zai taimakawa dalibai da kuma iyaye wajen cin gajiyar tallafin karatu wanda hankalinsu ma bai kai gareshi ba, don haka iyaye da dalibai sai a dage.
Allah ya bada sa’a.
Aimanakowadanja
Social media Strategies
23/12/2018
Follows
Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
13-12-2018.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment