Wednesday, December 26, 2018

2019: INEC ta sake bullo da dabarun magance magudin zabe.

A kokarinta na gudanar da sahihan zabuka da magance magudi da sayen kuri'u a shekarar 2019, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bullo da wasu dabaru na fasaha domin tattara sakamakon zabe da masu ruwa da tsaki zasu iya bibiya.
Kwamishinan INEC a jihar Benuwe, Nentawe Yilwatda, ne ya bayyana hakan yayin wani taro na masu ruwa da tsaki da jami'an 'yan sanda. A cewar masu ruwa da tsaki, amfani da sabuwar fasahar tattara sakamakon zaben zata kara wa zaben 2019 kima da karbuwa. Shugabannin jam'iyyun APC, PDP, LP, APGA da sauran su sun halarci taron bitar da aka yi a ofishin INEC na jihar Benuwe.

INEC ta samar da sabbin dabarun ne domin magance irin matsalolin da hukumar ta fuskanta a zabukan da aka yi na baya-bayan nan a jihohin Ekiti da Osun. Domin karin Bayani sai ziyarcide: https://hausa.legit.ng/1211514-2019-inec-ta-sake-bullo-da-dabarun-magance-magudin-zabe.html?fbclid=IwAR336o1w5-aJF5a16K_lNRTHzDgmMlCT0Z5fUXkAveKj15id7bQ8CaldKpM



Abu Aiman Danja
Social Media Strategies

No comments:

Post a Comment