Hanyoyi Ashirin (20) Da Zaka Bunkasa Kasuwancinka Ta Instagram
Digital Marketing Instagram
Make Money Online
Marketing
Online Business
December 20, 2018 Basheer Journalist SharfadiLeave A Comment On Hanyoyi Ashirin (20) Da Zaka Bunkasa Kasuwancinka Ta Instagram.
Hanyoyi Ashirin (20) Da Zaka Bunkasa Kasuwancinka Ta Instagram
Instagram shima kamar sauran shafukan sadarwa na internet ana amfani dashi wajen tallata haja, tunda dai malam dan Hausa yace mai talla shike da riba…
Kayi searching @jiffpom a instagram wadda take bayyana kanta a matsayin kare, amma yanzu haka tana da mabiya Miliyan Takwas da dubu dari biyar 8.5M a Instagram kuma tana cikin wadanda ke kan gaba wajen samun kudi a instagram.
Bara na kyale labarinta haka, Yau Ina tafe da hanyoyi guda ashirin cir! Wanda zasu taimaka maka wajen cicciba kasuwancinka a Instagram sai a biyoni sau da kafa.
1. Kayi bayanin kasuwancinka a Bio din account dinka, ka saka takaitaccen bayanin abubuwan da kake siyarwa.
2. Ka dinga neman mabiyanka suyi tagging din abinda ka saka, zaka ga idan masu tallan kaya a instagram sukayi posting suna rubuta “tag friend”.
3. Ka dinga neman irin wanda suke irin sana’arka a shafin kaga yadda suke nasu tsarin, kuma ka dinga tagging dinsu a post dinka, Da wannan hayar Kanny Wood suka mamaye Instagram a Arewacin Nigeria.
4. Ba ko yaushe zaka dinga posting akan kasuwanci ba, Ana son ka dinga yin posting na nishadantawa lokaci zuwa lokaci
5. Ka dinga yin Garabasa (Promo) kamar dai a lokutan azumin Ramadhan ko Sallah d.s.
6. Ka dinga tallata kayanka a comment din abokanka, Ka dinga shiga tattaunawar da ta shafi sana’arka.
7. Ka dinga yin “repost” na posting din mabiyanka, tamkar kana yaba musu hakan zai sa su dinga daraja kayanka.
8. Account dinka ya zama biyu personal mai sunanka da kuma na kasuwancinka yadda zaka dinga mentioned din kowanne.
9. Ka kaucewa yin duk wani posting da bai dace ba, na cin zarafi ko kuma na tada tarzoma.
10. Ka dinga yin posting na abubuwan dake da alaka da al’ummar da kake son su sayi kayanka.
ANYOYI GOMA DA ZAKA SAMI FOLLOERS A INSTAGRAM
11. Ka dinga taya followers dinka murna a duk ranaku kamar sabuwar shekara, da makamantansu.
12. Ka dinga amfani da HashTag na abinda kake siyarwa da Abinda keda alaka dashi da kuma yankin da kake.
13. Ka saka link din tallan kayanka a bio link.
14. Ka tsara rubutu da hotuna masu kyau wanda zasu ja hankali.
15. Ka saka location din inda kasuwancinka yake a Instagram din.
16. Ka sanya alamar kira (call) a account dinka.
17. Ka dinga saka link din kayanka a story. Da HashTag a story din.
18. Kayi amfani da salon siyar da kaya kyauta abinda mutum zai biya shine kudin kawowa, misali kayan N300 ne kudin kai masa kuma N150 to sai kace ga kaya yau kyauta kawai kudin kawowa mutum zai biya N500.
19. Ka dinga yin live video kana tallata kayanka alokaci.
20. Ka dinga biyan Instagram su tallata maka kayanka.
Allah ya bada sa’a.
Aimanakowa
Social Media Strategist
followed
Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
20-12-2018
No comments:
Post a Comment