Wednesday, December 26, 2018

JAM: ( YADDA ZA'A BUDE JAM PROFILE 2019)


Jamb: {Yadda Zaka Bude Jamb Profile 2019/2020}

Jamb Profile dai shine mutum ya samu mallakar account da shafin internet mai hukumar jamb wanda da shine zai yi amfani wajen yin register Jarrabawar.

A wannan shekarar Jamb din tasha ban-ban dana sauran shekarun baya da suka gabata inda a wannan karan koda kana da profile na shekarar da ta gabata to sai ka sake domin kuwa akwai wani code da za'a yi amfani dashi a jarabawar ta bana,  kuma ana samun code dinne bayan bude Jamb Profile din.

Yadda ake bude Profile din shine:
1. Da farko ka ziyarci shafin hukumar www.jamb.org.ng
2. Sai ka shiga "Login" zai budo maka sabon shafi.
3. Sai ka danna alamar "create new account"
4. Zai budo maka Inda zaka saka lambarka sannan ka amsa tambayar tsaro.
5. Daga nan sai ka danna "verify email".
6. Daga nan zai budo maka sabon shafi da zai fada maka cewa an tura maka sako email dinka.
7. Sai ka koma cikin email dinka domin tabbatar da sakon idan baka ganshi ba ka duba sauran folders.
8. Sai ka bude sakon ka danna link din dake ciki.
9. Zai budo maka sabon shafi da zaka cike abubuwa kamar haka:
a. Suna
b. Jinsi
c. Ranar haihuwa
d. Kalmar sirri (password)
e. Lambar waya
f. Kasa
10. Bayan ka gama shigar da bayanan sai ka danna "sign up" Shikenan yana budewa ka bude jam Profile dinka.

Idan baka da Email ka duba nan ga bayanin yadda ake bude email

Rubutuka Masu Alaka Da Wannan:


Allah ya bada sa'a

Abu Aiman Danja
Social Media Strategist.

No comments:

Post a Comment