IDAN KAINE YA ZAKAYI?
An turo ma wani Copper #198,000 maimakon a turo masa N19,800
Wani matashi mai yiwa kasa hidima a jihar Borno, da aka bayyana sunansa da Abu Bakr Bilyamin ya tura wa hukumar yiwa kasa hidima NYSC wasikar cewa, an yo masa aringizon kudi har naira dubu dari da tis'in da takwas N198,000 maimakon a turo masa naira dubu sha tara da dari takwas N19,800 na biyan alawus din wata-wata da hukumar ke yi masu yi kasa hidima.
.
"Zuwa ga NYSC, ina mai sheda maku cewa a yau 22-12-2018 an turo man N198,000 maimakon a turo man N19,800" kamar yadda ya rubuta.
.
Sai dai labarin ya jawo cece-kuce a yanar gizo inda wasu ke ganin wautarsa da ya nemi mayar da kudin, inda suke ganin tsuntsu ne ya fado masa daga sama gasasshe, a inda a daya bangaren wasu ke ganin ya nuna halin kwarai da ya mayar da hakkin da ba nasa ba.
Abu Aiman Danja
Social Media Strategies
No comments:
Post a Comment